🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍧🍹
*NA*
*_Ummieluff😘_*
&
*_Rash Kardam💕_*
Page
*36~40*
Candy tace "eh wallahi d'azu naga an wuce da motar gawa,amma bansan wani gida bane kawai sai mu gan-gara kasan layi in munga gidan sai mu shiga".
Munay tace "toh yanzu ta wani layi zamu fara neman gidan"? Gashi wlhy dama yunwa nakeji,kinga umma kubewa ta dafa koh alfarman wake babu,kwanciyan nan da kikaga inayi na bakin ciki ne" candy ta fashe da daria "kaji yar iska yanzu dabance miki anyi rasuwa ba, da ashe mutuwa zakiyi da yunwa,dan nikam na daure naci kwad'on garin kwaki". "Toh yanzu dai tashi muje". Munay ta janyo hannunta "ke tsaya kefa bakida wayo,yanzu idan umma ta tambayeki me zamuce"? Candy tayi shiru ta d'aga kai kamar me tunani."ammah fa kawata kin kawo shawara,toh yanzu me zamu ce da ita"? "Yauwa zo muje nasan mezan ce da'ita". Suka fito atare munay na kokarin saka hijabinta.
"Ummah bari muje mu gaida Asea B Aliu kawarmu mamanta bataji dad'iba jiya aka sallamota daga asibiti". "Eyyah toh idan kunje ku gaidata da jiki,Allah yakara mata sauki" atare suka had'a baki wajen fad'in"Ammen" sannan suka fice da gudu. "kai ammah kin taimakemu da yau umma bazata bari inje ko inaba" yanzu ta ina zamu fara kenan gashi bamusan gidan ba" kumafa, muje mud'an zagaya mugani". Haka suka rinka yawo cikin anguwan shiga nan,fita can har suka gaji basuga inda ake zaman makokin ba. Zama sukayi kofan wani gida ishin ruwa ya ishesu..sun rasa ina zasu shiga su samu ruwan sha.
Can saiga mai saida pure water.da sauri candy tace "me ruwa" da karfi cikin sauri ya iso wurin. Cikin kakkarfan murya candy tace "bamu na naira goma",ta d'auki d'aya tana kallon Munay"ke kina kallona bazaki sha bane" munay ta kalleta dan tasan cikinsu babu mai sisi, ammah yaya ta iya ta d'auki guda d'aya tasha itama. Yauwa jiramu anan bari mu karbi canji a wancan shagon, ta nuna masa wani bangare,kamin yaron ya juyo taja hannun munay suka kwasa aguje yaron na binsu, suna gudu har suka bace mishi da gani,yaja musu Allah ya isa.
Da kyar suka 'buya wajen wani gida suna nishi..Munay tace "ammah ke yar iska cefa,kisa musha ruwa ammah bamuda ko sisi"Ke dalla ja dagacan idan kikace zakisha abu sai kinada kud'i toh ashe zaki mutu wata rana". MunaY zatayi magana sukaji kukan wata mata daga gefensu ta wuce tana kuru'ruwa. Munay ta kalli candy suka had'a baki wajen fad'in laaa ga gidan da ake zaman makokin can. Suka kwasa aguje zuwa gidan, suna isowa kofan gidan sukaga gidane nagani nafad'a,anata shigar da drinks katin-katin..Candy ta rike baki jiki na rawa taja hannun Munay zuwa kofan gidan.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
0 comments:
Post a Comment