🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI* 🍧🍹
```Umieelurv
&
Rash kardam```
Page➖91-100.
Duk masifa da tsiwan da ta ɗago domin ta masa tana ɗaga kanta sukayi ido huɗu nan take ta nemi masifan ta rasa. Rass!!! Taji kirjinta ya buga arba da tayi da kyakkyawn saurayi, ajin farko wan da duk wata mace ke fatan samunsa. Wani sanyi ya sauka azuciyanta. OMG tafaɗa azuciyanta nan take ta sakar masa ta wani tattausan murmushi daya daɗa fito da kyawunta azahiri. Kafa mata kyakkyawan fararen idanunsa yayi sai murmushi fararen hakoransa suka baiyana. Candy wani daɗi ya mamaye mata zuciya dan bata taɓa tsammanin babban yaro kaman wan'nan zai kulataba,ga kyau ga kuɗi aina gama caɓawa arayuwa in siyama na sabon gida mai kyau nasan Ummana zataji daɗi.
*** ****
"ah'aaam" yayi gyaran murya wanda sai yanzu Canday ta dawo daga duniyan tunani data shiga. "Tunanin me kikene Beauty?." Wani daɗi taji da taji ya ambaci kalman beauty taji kamar ta saka ihu. Ina bakin Candy yaki rufuwa sai murmushi take, da kyar ta tattaro nutsuwanta "ah! ah!! Babu komai sauri nake shiyasa Ummana tana jirana." "Alright dear nima banso tsayar dake akan titi hakaba, sabida ba mutunci,ammah ganinki yasa nakasa juran tafiya ba tare dana miki magana ba" shiru Candyƴ tayi tana sauraron daɗin muryansa. "Toh yanzu dai ba wannan ba gidanku zaki nuna min sai anjima na dawo muyi magana na fahimta ko?". Cikin sauri Candy tace "eee'ee hakane" cikin sauri ta kwatanta mishi gidansu ko irin jan class ɗinnan babu taga mai kuɗi. "To sai anjima beauty inasha Allahu zanzo anjima inganki,ammah in bazaki damu ba muje mana in ajiyeki." Candy ta ɗanyi jim kaɗan sannan ta ɗago kai tana kallonsa "please beauty don't say no" ya faɗa cikin karamin murya. ahankali yafito daga motan yanzune taga zahirin kyawunsa tafiya yake cike da kasaita harya iso ɗaya bangaren tareda buɗe mata kofa " bismilla muje". Cikin sauri taje ta shiga motan wani kamshi ya bugi hancinta nan take ta lumshe idanunta... Sanyi takeji yana shiga jikinta gashi ta rasa ta inane wannan sanyi ke ratsata haka dube-dube tasama dan ganin inda sanyin ke fitowa. Tana kak'kare jikinta da hijabin dake jikinta,Tama manta tana tareda wani. ahankali ya furta "o'oo am so sorry beb bari na rage Sanyin AC da alama yana damunki" {haha su candy ba'a taɓa shiga mota me Ac ba lol!} Dai-dai kofan gidansu ya ajiyeta sukayi sallama ta fita daga motan tana tafiya ahankali su Candyƴ harda canza salon tafiya kallonta yake tareda dukan siterin motan da karfi yace "shez so beautiful, i think i've found my missin wyf" ahankali yake drivin harya bar layin.
"Assalamu Alaikum" Ta shiga gida da sallamanta Umma tagani tana soya kaji masu yawan gaske. Ihu ta shiga gidan dashi "eeee Ummana waya bamu kyautan kaji"? "Ah! Ah!! Khadija aikatau aka bani gobe akwai biki da za'ayi abayan layinmu, yaya kin dawo daga makarantan yaya karatu"?. "Lafiya kalau Ummu, amma yanzu dai yunwa nakeji wlhy ina abincina"? Da hannu Umma ta mata nuni da inda abincin yake. Candy na cin abincin tana kallon kaji da Umma keta faman soyawa. Can taga bazata iya jurewa ba tace "Umma kazan bazamu ɗan-ɗana bane"? "Kinga bana son sakarci kajin mutane ne zamu ɗan-ɗana toni badani ba wannan sakarcin". Candy taji kamar ta fashe da kuka dan bakin ciki har idanunta suntara hawaye,(kunsan idan mutum ya kwaɗaito da son abu ba'a bashiba yanda yakeji)Tana nan zaune kamar mage. Ummah najin an'kiran sallan la'asar ta mike dan zagayawa bayi. Candy na ganin haka ta isa bakin murhun taɗau cinya babba guda ɗaya. "keee Khadija me kikeyi abakin murhun"? Da sauri ta juyo "babu fa Umma kawai nazo gyara miki icen ne." "Muga hannunki!" Candy taki ta fara kowama baya ahankali "nace muga hannunki ko bakya jine"? Da sauri candyƴ ta arce ta gefenta aguje." Zaki dawo ki sameni".
*** *** ***
Misalin ```7:30pm``` wani ɗan almajiri yashigo gidan "Assalamu Aleikum wai ana sallama da bauti" Umma dake alwalan sallah isha'i tace " ayyah yaro ba gidan bane babu bauti agidan nan" mikewa yayi zai fita Candy tayi carap tace "aihoo Ummah nasan gidan su nan suke kwanan'nan suka kauro anguwan nan" bata jira ansan Umma ba taja hannun almajirin suka fice "zo in'nuna maka gidan" suna fita tana hango motan bata bita kan almajirin ba tayi wajen da sauri. Da sallamanta ta'isa wajen kamar abun kirki,ya ansa fuskansa ɗauke da murmushi. azuciyanta tace "wai wannan baya gajiya da murmushi ne? "Barka da zuwa Sarauniyar kyawa'wa" Tayi ɗan murmushi "barka dai ina wuni" Ta gaidasa, "Shigo mana daga ciki" har tayi kamar zata shiga sai ta tuna da sanyin da ke shiga jikinta ɗazo sanda taji ɗan mura-mura. "a'a nan ma yayi wlhy" fitowa yayi daga motan cikin wani lal'lausan farin shadda wanda yaji zubi kamar bada kuɗi aka yisu ba. tsayawa yayi daga gabanta yana murmushi "as u wish ma beauty" "Kamar dai yanda nafaɗa miki ɗazu ina ganinki naji kinyi min,da farko dai ni sunana Abdoul-wahab ina zuwa garinnan tym to tym dan duba yan uwana, Ah Abuja nake aiki ni Manager bank ne FCMB wato first city monument bank, ina shigowa garin nan dake nasoma arba sai naji ajikina lalle na samu matar aure. Idan bazaki damuba zansu sanin wacece ke"?. Cikin muryanta mai matukar sanyaya ran mai karatu tace "sunana Khadija,ammah amfi sanina da Candy". "Woaw!!!" Ya faɗa yana mai tafa hannu tattare da murmushi "what a nice name Khadija". Yanda ya furta sunan yasake sa Candyƴcikin wani shauki. Nan dai taɗan labarta masa labarinta. "Toh Khadija bana son rikeki da surutu da yawa dan naga 8:00 yawuce yanzu kozan iya samun number ki"? Cikin sauri ta ansa "banida waya fa". "toh babu damuwa beauty insha Allahu zan samo miki waya wanda ya dace dake". Cikin motan yakoma miko mata kuɗi yayi wanda tunda take bata taɓa ganinsuba balle harta rike irunsu, nan take hannunta yaɗau rawa kamar mazari. "karbii mana beauty" Sa hannu tayi carap har tana yakushinsa da kyar ta tat'taro yawun bakinta da nutsuwar ta kamin ta iya furta "nagode".
Tana shiga cikin gidan ta ɓoye kuɗin cikin zaninta. "Aww harkin dawo hala gidan da nisa" "Eee" kawai ta ceda Ummah. Sannan tabi lafiyan gado lumshe idanu tayi tana kallon kayatac'cen murmushinsa wani ihu ta saki tareda rungume pillow a'hankali ta furta wannan shine ```Mr Smiles•```
Kuci gaba da kasancewa tareda mu😘
*TAGWAYEN MARUBUTA*
0 comments:
Post a Comment