New Post

Monday, 27 February 2017

BAZATA PAGE 3

BAZATA

By

©Rash Kardam

                     
Aiki sosai yayi kafin ya fara ganin marasa lfy, sai da ya gama iya wanda zai duba su a ranan kafin, ya taso yazo ya kwanta kan resting chair, dake office din ga wani kamshi da yake tashi hade da sanyin A C, ko da ya kwanta lumshe idonsa  yayi nan take abunda ya faru tsakaninsa da Jidda ya dawo masa, sai da yagama tunaninsa kafin ya saki wani mugun murmushi, sai kuma ya soma tariyo abubuwan da yasasu rashin jituwa, watani kadan da suka shude wata safiyar monday ya yi lade gun aiki gashi da marsa lfy da zai duba, gudu yayi a mota sosai kafin ya iso asibiti cikin sauri ya dauki briefcase dinsa, sauri yakeyi sosai, ya shigo asibi, ya shiga emergency, da sauri sauri yake hawan stairs, bai lura da wacce take zuwa ba, saiji yayi ya bude mutun, da sauri ya dago sai da yaji gabansa ya bada dam…. Madadin ya bata hakuri sai yakasa, sai wani mugun kalon da yabita da shi tare da cewa ke bakya ganine, cikin tsananin mamaki take kalon sa, tace kodai kai baka gani dai, wani saki ya saki Mtss yayi gaba abunsa, wannan abu ba karamin bata ma jiddah rai yayi ba amma ta share, ta koma cikin pharmacy dinta taci gaba da bada magun gunanta, tunda wan abu ya faru basu sake haduwa ba ita harta manta da shi, sai ranan ga wata maras lafiya tazo gurinta sayan magani, nan ta duba ta kardan sai ta karanta magun gunan, kafin ta dago ta kalli maras lfy tace waya rubuta miki wa yan nan magungunan, maras lfyn tace bansan sunansa ba amma naji kamar suna cewa wai Dr Ghali, haka kurum ana ambatan sunan sai da taji gabanta ya fadi, duba sign din tayi, haka kurum taji rubutum ya burgeta, ta kalli matar tace a kwai maganin da ya rubuta miki kuma zasu miki karfi, baki kai matakin shansu ba don haka zan canza miki da dai dai naki, matar tace to nan ta debi magun guna ta canza mata su, ta tafi matar. Itakuma taci gaba da sabgar gabanta.
Ko da matar ta kai ma Dr Ghali maganin cikin bacin rai yace wacece take da daman da zan rubuta magani har ta canza acikin asibitin nan? Wacece ita? Har take gwada bansan mai nake ba? tayi kadan ciki fushi ya ce wa matar tana ina tace tana cikin pharmacy din yace muje, suna isowa bai tsaya ganin wacece ba idon sa ya rufe,
Jiddah ko kanta na sunkuye tana latsa wayarta, sai ji tayi ana buga table din gabanta, kee  wacece acikin Asibitin nan da har zan rubuta ma gani ki canza, zaki gwada min ban san aiki na bane, wacece ke?, mai kike takama da shi? sai a san nan ta dago kanta don ta ga wanene wan nan, dan rainin sense din dayake mata hayaniya, cike da tsiwa ta dago nan sukayi 2 eyes  dashi cikin bacin rai tasoma gamana.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts