°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*14*
_Kwanaki sun tafi Jiddaga tayi wayo sosai har tana takawa magana kuma tana kab'awa rabin yininta gun Fatima ke kula da ita don tana son 'yar tamkar 'yar cikinta ita ma Jiddag ta shak'u da ita sosai Aisha hakan da Fatima ke nuna na d'iyarta k'auna ba k'aramin dad'i takeji ba hakan ya k'ara musu dank'on zumunci da k'auna. In har Aisha da Mijinta sun zo godiya akan kula da 'Yarsu da takeyi Malam da Fatima su ce" karku da mu ai *'YA'YA DA DUKIYA BA'A K'ETARSU* baka san wanda zaka mora ba bakasan wa zaiji k'an ka ba kuma au duk mun dawo d'aya". Wannan kalaman yana k'ara masu Aisha da Malam Jibrin jin k'aunan mak'ocinsa don duk wanda yaso d'an cikinka ya gama maka komai._
_Yau Fatima ta tashi da matsanacin zazzab'i ga yawan tashin zuciya hakan ba k'aramin tayar ma Malam Ahmad hankali yayi ba hatta Jiddah da take k'arama tarasa gane kan Aunty tan. Haka ta yini Malam yaso suje Asibiti ta ki ta ce "hala mura ne ya had'u da zazzab'i zata sha magani kawai". Zuwa dare jiki yaki hausa hankalin Aisha da Mijinta ba k'aramin tashi yayi ba ganin lokaci d'aya tayi wanni mugun rama Malam Ahmad shi ya d'aga ta suka shiga motan Malam Jibrin suka nufi Asibiti nan likitoti sukayi kanta suna bata tai makon gaggawa._
_Malam Ahmad kasa zaune yayi sai zirya yakeyi Jiddah kuma sai ihu take yi sabida yau sam bata zauna a hannu Fatima ba kuma ta saba da ita jikin Jiddah yayi zafi sabida kuka a haka Aisha ta samata nono a baki har baci ya d'auketa sai sauk'e ajiyar zuciya take yi._
_Wata likita ne ta fita da sauri Malam ya taso don ya mata magana bata tsaya ba ta wuce sa da gugu ta sake dawowa ta wuce cikin sauri ta shiga emergency Malam na ganin haka hankalinsa ya k'ara tashi addu'a kawai yakeyi a cikin zuciyarsa ana haka likitan ya fito fiskansa babu wani annuri yana goge fiskansa cikin sanyin murya ya ce"ina 'yan uwan wannan maras lafiya waye mijinta?". Damm!! K'irjin Malam ya buga cikin fargaba da tsoro ya ce" gani nan". Tare da mik'ewa ya nufi gun likitan._
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment