New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 1-5

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧

                            *Na*

*Ummieluff*
          *Rash Kardam*

_Bissmillahi rahmanu rahim_
_Dukkan yabo ya tabbata ga ubangijin sama da k'asa, mai raya kuma mai kashewa_

              *Tsokaci*
_Wanna labari k'agagen labari ne munyi shi sabida abunda yake faruwa a wannan zamani namu a gidan rasuwa, in har yazo iri d'aya da labarin ki/ka to sai ku gyara ba wai dan tozarci mukayi ba sai dan samun gyara aciki al'umma. Ya Allah muna rok'anka ka bamu ikon farashi mu kuma gama lafiya Amin._

*Gamasu gyara k'ofa a bud'e take muna sauraronku don ko da yaushe mu masu kuskure ne sai fatan Allah ya yafe mana kuma muna maraba da masu na gyara.*

            *Jin-jina*
   ```Jin-jina da duk wata k'ungiyan``` *```ONLINE HAUSA WRITERS```* ```muna k'ara gode muku da jin-jina muku gurin k'ara d'aukaka rubutu da jajurcewa gurin kare marban rubutu da hausa Allah ya k'ara d'aukaka da basira Ameen.```
*```NAGARTA WRITERS ASSO```*
*```FIKRA WRITERS ASSO```*
*```EXCELLENT WRITERS```*
*```ONLINE HAUSA WRITERS ```*
*```WISDOM HAUSA WRITERS ```*
*```EXTREME HAUSA WRITERS```*
*```WRITERS WORLD ASSO```*
```Allah ya k'ara maku d'aukaka da Albarka Ameen.```

Page
*1~5*

Matashiyar narinya na hango bak'ace tana sanye da hijab mai ruwan madara kalo d'aya zaka masa ka gane ya d'an kwana biyu. Yarinya bak'ace tana da d'an tsayi ko damuka kalli fiskanta tana da madai-daicin fuska tana da dogon hanci tare da k'aramin baki sai fararen hakwaranta dake haskawa kalo d'aya zaka mata ka gane nutsuwar da ke tattare da ita tubarkalla mashaa Allah abunda mukace kawai. Cikin sauri naga tunifi gidansu Haneefa da ke Tudun wada hausawa road da sallamanta ta shiga nan ta tarar da Auta tana zaune a gefen Hajiya cikin girmamawa ta gaida Hajiya. Da sakin fuska Hajiya ta amsa ta zauna a gefe Candy ta ce"Auta wai ni sai yaushe zaki rage son jiki". Auta ta murmusa ta ce“ sai randa zan girma kamar Aunty Haneefa". Candy ta murmusa ta ce“ah! Lallefa da sauran aiki kenan". Hira suke yi da Hajiya da Auta da Candy. Amrah da K'urratu~ayni suka shigo bayan sun gaida Hajiya suka zauna.
Hajiya ta ce“ya na ganku duk kunyi jigum". Kurratu~aini  ta ce“hmm rasuwa akayi anan balayin bayan mu layin 'yan kosai". Hajiya ta ce“innalilahi wa inna ilaihi raji'un waye ya rasu haka?". K'urratu~ayni ta ce“Malam Idris na gidan su Sa'idu". Hajiya ta ce“ayya Allah ya jikansa da rahma". Suka amsa da amin Candy na jin haka ta mik'e da sauri ta ce“Hajiya zan tafi sai anjimanku". Cikin sauri ta fito ta nufi layin 'yan kosai da ke bayansu cikin sauri ta nufi anguwan tun daga nesa ta hango mutane zaune ga kulolin abinci wanni sassayan ajiyar zuciya ta saki tana zuwa rumfa da ake karb'an gaisuwa ta k'ak'alo hawaye ta farayi ta rusuna ta gaidasu tukun ta mik'e ta shiga cikin gidan tun daga nesa ta hango drinks kala-kala a jere ga kulolin abinci wasu na ci wasu na shan juice yayin da wasu ke d'aki sai hira suke yi suna shewa tamkar ba a gidan rasuwa suke ba, a haka ta k'ara ta saki kuka a dai-dai k'ofar shiga d'akin tana zuwa ta fara kuka ta na gaida mutane nan suka amsa bayan ta musu ta'aziyya ta ja gefen wata mai cin abinci ga namomi akai tamkar a gidan biki take. Candy sai da ta hadi'yi miyau don yanda k'amshin ke bugan hancinta. Pherty ce ta fito ganin yanda Candy ke kallon mai cin abinci ta ce“bai war Allah zo ki karb'i sadakan abincin kema". Cikin sauri Candy ta mik'e sukaje gaban kulolin abincin Pherty ta ce“mai kike so a saka mik?". Candy sai raba ido take ga taliya, ga shefe(shinkafa), ga tuwon shinkafa miyar taushe. Candy ta ce“asa min shinkafanan". Nan Pherty ta zuba mata tare da nama zuk'u-zuk'u Futha da Ummu Abrar suka iso gun d'auke da wani manyan plate kai ka d'auka su goma zasuci abincin. Jellop d'in shinkafa suka saka tare da nama kamar zai yi magana ga kifi tukun suka d'au juice zasu tashi Candy ta ce“ku d'an k'aramin naman nan da juice d'in ba musu suka k'ara mata tukun suka nufi wani rumfa suka zauna suna ci suna zuba hira tamkar ba gidan rasuwa ba.

        *_TAGWAYEN MARUBUTA_*

Coming soon....

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts