New Post

Monday, 20 February 2017

DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI PG 31-35

🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
             DAI-DAI RUWA
              DAI-DAI GARI
   (DON'T EXPECT TOO MUCH 
                         IN
                       LIFE)
🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓

                         NA

©RASHIDA .A. KARDAM

Pg-31~35

Ko da ta iso falo turus tayi da ganin Abban Yusrah, ba karamin girgizatayi ba, gefe tasamu ta rakube kamar munafuka. Abban ta yace"Hajiya da Maman Yusrah tazo mai tace miki?. Nan hajiya ta fad'i komai,  idon Ummin Yusrah ya kawo kwalla, nan tafara hawaye Abbanta yace"yanzu abunda zaki mana kenan tarbiyan da muka baki kenan?. Cikin bacin rai yayi kanta yasoma kifa mata mari da gudu tazo bayan Abban Yusrah ta buya, hakuri yasoma ba ma Abba. Tukun ya zauna yace"kayi hakuri kasan halinmata.
"Ka dau matar ka ku tafi dan Allah kayi hakuri ka maidata.
Abban Yusrah yace"bakomai Abba na maidata Allah ya kare faruwan na gaba duka suka amsa da Ameen. Hajiya tace"ki je ki debo kayanki ki bi mijinki don yau bazaki kwana a gidan nan ba. Sum sum ta mike ta tataro kayanta ta dauko Yusrah ta fito falo. Sallama suka musu suka tafi.
A hanya ko Abban Yusra ko ya kalleta, ya daure fuska sai shan kamshi yakeyi. Haka har suka iso gida dakinsa ya wuce bai tanka mata ba.
Kwanata biyar da dawowa ya fita sabgarta gashi tayi nadaman abunda ta aikata, tanaso su shirya amma ba fuska. Hakan yasaka ta kira Munay ta fada mata komai, sai da Munay ta mata nasiha kafin ta bata yan shawarwari.
Duk shawaran munay tabi cikin ikon Allah tashawo kan abunta yanzu, zaman lafiya sukeyi kamar basu taba samun matsala ba.
Su Hameeda kuwa basu samu zama ba don shirin bikin Khairat wanda yau ne daurin aure, duk wani shagali anyi shi, da yamma aka daura aurenta akan sadaki naira dubu d'ari. Da dadare aka kai amarya gidanta suka wuce dinner, bidi'a kam ansha a bikin sun cashe. Kawaye da yan uwa sun watse sai fatan zaman lafiya ma amarya.
Hameeda kuwa salon iskanci kala-kala take ma Haisam, shikan har ya sima hakura da halunta.
Gidan Amarya kuwa kidane ya canza, don duk yanda halin ango yake a waje, to abun ba haka yake ba, duk kayan da ya mata na akwati ya kwashe  su ya sayar wasu ya mayar wa masu shi, asai aro yayi. Hatta wayarta ya kwace ya biya bashi dashi, randa Hameeda taje taji labari ta tausaya mata sosai. Khairat tace"Hameeda ina shawarta ki da ki rike Haisam da *AMANA* kinga darasi akaina son abun duniya da k'arya ga abunda ya jawo min. Hameeda tace"tabbas naga darasi kuma zan basa hakuri. Ana cikin haka sai ga Saleema tazo gidan fuskata dauke da damuwa, Khairat tace'Saleema lafiya na hanki haka?.
Saleema tace"ina lafiya fa, ina sairayin da ya min kayan sallah, kawai yaga wayan da TJ ya sai min IPhone din nan.
"Yace in basa zai canza min babbanta. Sai dana basa bayan ya tafi yamin text message. Yace"ke wata irin mara hankali ne da zanta kashe miki kudi a banza ne.
" na tafi da wayarki ta isheni kudin dana kashe miki har da saura.
Salati suka saka duka nan sukayita jimamin abun kafin suka tafi gida.
Hameeda tun daga wan nan lokaci ta kira Haisam ta basa hakuri, suka shirya yanzu soyayya mai tsabta suke guda narwa ba karya aciki don taga darasi akan kawayenta, sai yanzu ta yarda da kalman baushe dake cewa *DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI* sannan kar ka saka buri akan abu ko kwadayi da yawa(don't count your kitchen before the hatches).
Yan uwa masoya littafina nan na kawo karshen wannan karamin labari ina fatan kun dau darasin dake ciki. Ina kuma muku barka da *SALLAH* Allah ya mai maita mana ameen. Allah yasa ibadun mu karb'ab'iya ne Ameen.
      *HAPPY SALLAH*

          *ALHAMDULILAH*
Duk yabo da godia sun tabbata ga Allah ubangiji sammai da k'assai. Da ya bani ikon kammala wannan littafin lafiya.

              *TA'AZIYYA*
A madadin dukannin member group d'in *RASH KARDAM HAUSA NOVELS* 1,2,3. muna mik'a sak'on *TA'AZIYYA* mu ga iyalai da yan uwan *Fans* d'in mu *BARIYYATU HAYATUDEEN HAMZA( B. HAYYAT)* Allah ya jik'anki ya haskaka kabarinki, yasa Aljannah ce makomarki Ameen, da dukan *MUSULMAN* da suka rigamu gidan gaskiya Ameen. Mu kuma in tamu tazo, yasa mu dace da k'arshe mai kyau Ameen.

*IYAYENA ABUN ALFAHARINA*

Iyayena abun alfaharina a ko ina daku nake tin kaho, Allah ya barmun ku
Alhaji Abdullahi Yunusa Kardam da Hajiya Khadija Aliyu.

        *SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafi ga dukan masoyana da yan uwa da abokan arziki a matsayin goron Sallah. Sai kunjini a sabon littafina mai suna *~GIMBIYAN KARDAM~*.
      
          *GAISUWA*
Sakon gaisuwa ga dukkan *ONLINE HAUSA WRITERS* da fatan kunyi Sallah lafiya Allah ya mai maita mana Ameen.

            *KAWAYENA*
Kuma ina muku barka da Sallah.

             *GODIYA*
Godiya ga group din
WISDOM HAUSA WRITERS
BEST HAUSA GROUP WRITERS
EXTREME HAUSA WRITERS
GALAXY HAUSA WRITERS
MODERN HAUSA WRITER

              *DOLE NA YA BA MUKU*

*RASH KARDAM HAUSA NOVELS 1,2, n 3. Nagode da kulawarku gareni.

  *TALLAN SABON NOVEL 'DINA MAI TAKEN SUNA*

        *GIMBIYAR KARDAM*
Ya nan tafe ba dad'ewa ba Littafin da ya kushi Kiyayya tare da soyayya, ga  tausayi ga cin *Amana*  da kuma *Yaudara* duk ga tsan-tsan kishi, Hassada gamida kyashi duk a cikinsa. Makaranta kar kusake a baku labarinsa.
Yana nan tafe *~GIMBIYAR KARDAM~*

TAKU  A KULUM MAI QAUNAR KU.
*RASH KARDAM*

1 comment:

Popular Posts