MOTAR KWADAYI
Rash Kardam
31-35
Janyo ta yayi jikinsa, nan yafara sarrafata son ransa, niko ina ganin haka na yi waje. Sai da kusan 12 ya tashi a kanta, bayi yashiga yayi wanka ko wankan tsarki baiyiba, ko dayake ina ma ya iya d'in, Safiya kuma bakin ciki ya isheta, duk irin murzata da yayi son ransa amma ya tashi ko ya taimaka mata mtss tayi d'an guntun tsaki. (Niko Rash nace"bakiyi tsaki ba tukun, in dai namiji ne, kuma har ki basa darajanki, da kimarki, da martabanki, ae dole kiga wulakanci. Bare shi namijin duniya da yasaba d'an d'ana mata, ya kuma keta musu haddi, sai dai kiyi hakuri tunda ke mai KWA'DAYI ne ae ki wahala, daman hausawa sunce duk wanda ya hau MOTAR KWADAYI, zai sauka a tashar wulakanci. Safiya yanzu kika fara karo ma tukun indai bariki ne). Da kyar ta mik'e ta shiga bayi, tayi wanka tana fiwowa, ta soma jinsa yana waya da wata, jin alamun ta fito ya kife wayar. Jiyowa yayi fiskansa ba yabo ba fallasa yace"kin fito? Ga magun-gunan kisha, ya d'auko wani kud'in ya kara mata, ni zan fita in kin gama kya iya tafiya, sai na nemeki. Bai jira amsanta ba ya fita abunsa, bakin cikine ya isheta, yanzu haka hala gun wata ma zaije, juyawa tayi ta kali kud'i da ya ajiye, ta tuna dana jiya sai taji sanyi, yau tasamu abunda take so, don tunda take, ba saurayinta da ya tab'a matakyauta irin haka. Abinci taci ta sha magani, sai karfe d'aya tafito, gifan Seema ta nufa, tana zuwa ta ganta, da shisha a gabanta, sai zuka takeyi, shewa sukayi suka tafa, yar duniya, kinci dubu, Safiya ta juya ido, tare da rausaya su, cikin yanga tace" sai ceto, sai ni d'aya tamkat dubu. Tafawa suka sakeyi, nan taba ma Seema labari, Seema tayi guda eh lallale, ina miki murna da shigowa system, yanzu zaki san meye love. Ko bakiyi dan kud'i ba zakinima dan kashe KWA'DAYI, tafaa suka sakeyi, nan suka k'irga kud'in naira dubu tamani cuss, dubu goma taba ma Seema, ta mata sallama ta nufi gida.
�Da sallama ta shiga gida tana fara'a, yau tayi samuwa, a hankali take tafiya, sabida har yanzu kasanta na mata zafi, Malam ne ya fito da sauri, Yace"kee ina kika fito?. Sai wani yatsina take, kafin ta bashi amsa Innanta ta fito, ah ya haka?. Zaka tsaren 'ya da tambaya, ka aike tane?. Da kake tambayanta, ina ruwanka, da in da ta fito, tsaban takaici, Malam kasa magana yayi, sai zucyarsa dake masa suya, hannu yasa ya dafe k'irjinsa, da kyar ya shiga daki.
Inna ko suna shiga d'aki, Tace"Safiya ina kika je?. Bata amsa ba kud'i ta ciro ta mika mata, Inna ido ta zaro, tace" Safiya ina kika samu kud'i haka?. Murmushi tayi tace"wani saurayi nayi, shi ya ban kuma yana da kud'i sosai, Inna tayi shewa tace"a'a ah kirike shi da kyau, in dai zaina bamu, kinga num huta, Inna ta jirga kud'in, Tace"wannan Yaro d'an arziki ne, har dubu saba'in, Safiya tace" dubu tamanine ma, naba ma Seema dubu goma, sabida ta sanadinta ne, eh kin kyauta, Inna rawa tafara na murna,har ta manta da Safiya ba'a gida ta kwana ba.
Safiya kuma tace" washh barin d'an kwanta na huta.
Ayshat sanye cikin katon hijab d'inta, tana tafiya cikin ni tsuwa, tun daga nesa Khaleel ya hango ta, ganin ba mutunci bane ya tsareta a hanya, sai ya fara binta a baya, har sai dayaga tazo, zata shiga gida, Assalamu'alaikum ya mata salama, da kamar bazata amsa ba amma sanin muhimmanci sa, ta amsa, bai war Allah, dan Allah karki tafi ki saurare ni, jin ya ambaci sunan Allah yasa ta juyo, kanta a kasa, cikin hikima ya fara mata magana tare da gabatar da kansa, ni sunana Ibrahim Kabir, amma anfi kirana da Khaleel, tunda na hango ki zuciyata ta yaba da nutsiwarki, suka sace zuciyata, na taho da k'ok'on baran Kaunata ko zata samu matsuguni a zuciyarki. Sai da ya kai aya ta d'ago a hankali, sanye yake cikin kayan Copper yayi matukar kyau. F
Friday, 24 February 2017
Home »
» MOTAR KWADAYI PAGE 31-35
MOTAR KWADAYI PAGE 31-35
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment