HANNUNKA MAI SANDA?.
Sanah S Matazu
Rash A Kardam
8
Zaune take a madai-daicin falonsu wanda yasha gyara da kwalliya ga wani kamshi na musamman da ke tashi. Karatune ke tashi a falon daga tashar Sunnah TV.Can suka katse suka sako bayani kan layya ta yi tsit tana sauraro. Kalo ?aya zakai mata ka gane hankalinta kwance yake bata da wata matsala a rayuwanta.
?Assalamu'alaikum".
�Kamal ya yi sallama fiskansa ?auke da fara'a.
Naja cikin farin ciki ta tashi daga kishingi?an da tayi. Tare da kallon fiskan mijinta ta sakar masa da wani tsadaden murmushi mai narka duk wani zuciyan masoya.
?Amin Wa'alaikumusalam ya farin cikina, madaran zuciyata, abun alfaharina masoyina uban 'ya'yana angon Naja'atu".
Kamal ya sakar mata murmushi mai kayatarwa.
�Cikin tafiyarta mai d'aukan hankali ta iso gabansa tana aika masa da sakwaninta mai sanyaya masa zuciya. Hannunta tazaga ta bayansa tare da sakala shi a kunkuminsa ta kwantar da kanta a kafa?ansa suka tako har zuwa tsakiyar falon. Zubewa suka yi a tsakiyar falo tana mai masa sannu da dawowa cikin kulawa da dabara ta zame jikinta daga nasa, fridge taje ta ?ebo ruwa mai ta kawo masa tare da bashi a baki sai da yasha ta ajiye cup ?in.
Hira suka fara irinta masoya masu kulawa da junansu.
?My luv albishirinki".
Kamal ya fa?a fiskansa ?auke da tsantsar farin ciki.
Naja ta yi har da ido tare da juyasu ta kara narke masa a jiki ta kanne ido ?aya,
�?goro mai sanyina".
�Naja ta fa?a gyara zamansa ya yi tare da kara mannata a jikinsa ya ce,
?kofar Allah tafi ta shale, kuma duk wanda ya kasance mai gode ma Allah a kodayaushe to zai kara masa _La'in shakartum la'azidannakum wala in kafartum inna azabi la shadid."_�
Sai da ta juya ido ta ce,
"wannan haka yake mai sanyina".
Kamal ya cigaba da ce wa,
?kinga bamu ta?a tsammanin za'a bamu ku?in hutun mu nan kusa ba, cikin ikon Allah ba zato ba tsammani sai ?azu muka ji alert...".�
?MASHAA ALLAH!ALHAMDULILAH!! Nayi matuk'ar farin ciki Alhamdulilah! Allah ya kara rufa mana asiri amin".
Kamal ya cigaba da ce wa,
?kafin na shigo mun ha?a kawunan mu zamu yi tan-tan (Bauchi) watanda (Kanowa) kamowa (Katsinawa)na layya da wasu har mun bada ku?in".
Naja ta ?ago tana masa kallon mai ?auke da tambayoyi gaza hakuri ta yi ta ce,
" daman ana iya yin layya mutane da yawa ne?".
Kamal ya ?ago da fiskansa ?auke da murmushi ?ya girgiza mata alamar eh! Ya ce
"Tabbas wanna ba karamar tambaya bace Naja'atu kuma naji da?in tambayan, so ake musulmi ya zama da zaran wani abu ya same shi ya san yadda zai warware al'amurra akan karantarwar Annabinshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Bai halatta sama da mutum guda su taru akan rago ko tinkiya ko
taure ko akuya ba, amma ya halatta mutane biyu zuwa bakwai su hada kudi akan sa, ko saniya, ko rakumi, ko rakuma, domin su yi
layyah".
Ya karasa maganan yana kalon fuskanta.
Kai ta girgiza alamar ta gamsu,
"gaskiya ina alfahari da kai na kasancewa miji a gareni in Allah ya bamu 'ya'ya gaskiya zamu aurar da ita ga kowa ba sai masamin addinni".
Yana murmushi ya shafi kanta ya ce
"nima ina alfahari da ke Allah ya yi miki albarka".
Naja ta amsa da,
"amin".
Cikin kauna ya ce
"rufe idonki".
Ba musu ta rufe tana murmushi,
"miko hannunki".
Hannunta ta mika masa wani ?an akwatin ?ankune ya mika mata tare da tsaban ku?in naira dubu biyar.
Yana murmushi ya ce,
?bu?e idonki".
A hankali ta bu?e duk ras! Ta sauke su a kan hannunta nan taga ?an kunne fuskarta ta ?ago da niyyar magana ya tari hanzarinta ta.
?Wannan naki
0 comments:
Post a Comment