HANNUNKA MAI SANDA........
Sanah S Matazu
Rash Kardam
(4)
Cikin hikima Lubabatu ta dinga janta da hira tana yi mata nasiha har suka gama aikin.Suka yi sallah suka ci abinci, da zata fito ta sake jaddadamata taje taba mahaifinsu hakuri harta kai kofa ta dawo ta dubeta da kulawa.
"Ya akayi Janah?".
"Aunty an yanka ta tashi,baki gayamun ba mace tana layya nima in na girma na sami ku?i in yi".
"Janah manya,aiba a samun ku?i haka sidan sai kinyi sana'a kin dogara da kanki".
"Aunty ai zan soma sana'ar Yaya Sa'adatu bata da kyashi zata koyamun ?inki hakama Yaya Maryam,nidai kigayamun mace tana layya?".
Murmushin nasara ya su?uce mata ta ce,
"Janah! Mace na layyah domin duk abinda shari'ar musulunci ta zo da shi ba banbanci tsakanin mace da namiji sai abinda dalili ya banbance,saboda haka ya halatta mace ta yi layya kuma mijinta ya yi idan yana da hali hakanan 'ya'yanta, domin layyah ba biki bace ibadace da ake baiwa mutum lada idan ya yi kamar yadda akace ya yi kuma ya yi shi domin Allah,kenan yana da kyau maza su sani iyalansu ba gasa suke da su ba, ibadace da Allah Ya shar'anta ta akan maza da mata".
Cikin murna tayi tsalle tana fa?in,
"na gode Aunty Lubie".
Shigowar Najjash da gudunsa yasa suka hau tambayarsa abinda ya faru,cike da murna ya ce,
"Mamanmu an siyo mana rago".
Yana rufe bakinsa mahaifinsa ya shigo,hannunsa janye da raguna guda biyu suna kuka.Cikin murna ta tayashi suka ?auresu Murjanatu na gefe a ranta tana fa?ar ubangiji ya horewa mahaifina kodan ya sami ladan layya shima.Muryar Lubabatu ta katsemata tunanin.
"Abban Najjash ina muka sami raguna har biyu?".
Murmushi ya yi ya ce,
"wallahi Lubabatu yin Allah kawai wajan aikinmu aka raba mana guda-guda cikin ikon Allah kuma aka yi albashi yau.To muntaho hanya sai wanda akaban mota ta bigeshi ya karye kuma ka'ida kinsan ba a yin layya da me karaya shi ne na fidda cikin albashi na siyo wani".
Jinjina kai ta yi ta ce,
"tabbas hadisi daga Barra'u ?an Azib Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Ba'ayin layyah da gurguwa wacce gurguntakartta ta a fili take, hakanan da mai ido ?aya wacce hakan a fili yake (ina ga makauniya baki ?aya?), hakanan da mara lafiya wacce rashin lafiyar tat a a fili yake, hakanan da kyamusassa wacce take bata da mai. Hakanan Aliyu bn Abi Talib Allah ya kara masa yarda, ya ce:
''Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya umar ce mu da musa ido sosai akan idanu da kunnuwa, kuma kada muyi layya da mai yankakken kunne ta fuskar tsawo ko fa?i na kunnen.Timizi ya ruwaito hadisin 1498 , duk wannan idan ya bayyana kamar ?aya bisa uku,dukkanin wa?annan bayanai suna nuna mana itafa layya ibada ce yadda ake so zaka yi, ba yadda kai kake so ba,tabbas kayi tunani mai kyau ubangiji yasa mugani lafiya".
"Amin mace tagari".
Cikin murmushi Murjanatu ta yi waje tana sha'awar wannan ma'aurata masu kulawa da junansu.Tana shiga gida ta samu Mama dasu Maryam jigum-jigum da alamu har zuwa lokacin abinda ya faru na mintsinar zukatansu cikin sanyin jiki ta zauna tana dubansu.
"Mama kiyi hakuri da abinda ya faru,nasan Auntynmu bata kyauta ba".
Ga mamakinta murmushi Maman ta yi ta ce,
"babu komai Murjanatu na godewa ubangiji da kika fuskanci kuskuran mahaifiyarki amma bance hakan yasa ki rainata ba.Uwa-uwa ce a ko'ina daraja gareta koda ta buzuzu ce.
Tun ranar farko da Allah ma?aukaki ya halicci mutum ya sanya jagorancin 'ya'ya a hannun iyaye wanda yake shi ne uba na farko Annabi Adam (a.s).Wa?annan hakkokin an yi bayaninsu a wasu ayoyin na kur'ani mai girma, aka kuma ha?a tauhidi da biyayya ga iyaye domin nuni zuwa ga girman wa?annan hakkoki a fa?insa ma?aukaki;"Kuma yayin da muka riki alkawarin
Monday, 20 February 2017
Home »
» HANNUNKA MAI SANDA PAGE 4
HANNUNKA MAI SANDA PAGE 4
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment