🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍧🍹
```Ummieelurv😘
&
Rash kardam```
Page➖111-120
Misalin 8:00am Candy na bakin gate na makarantan su tun daga nesa tasan yau zataci duka sabida tayi latti. Malam Muh'd ta gani da wani zabge'gen dorina yana dukan ɗalibai, tun daga nesa ta soma tafia a karkace tana matse cinyoyinta da alama fitsari takeji sosai. Abun har daria ya bamu. _Kneelin down_ aka saka su ammah na Candy dan rashin kunya samun qaramin dutse tayi ta zauna akai babu wanda yake kallonta. Layi'layi ake dukansu har akazo kan candy nan take jikinta ya ɗauki'rawa idanunta suka canza launi nan take hawaye yasoma zubowa. " kee ni kikeson inzo inda kike da kaina ne"? Cikin saurin Candy ta mike sai ganin dutse yayi a bayanta "owk wato gaki mai wayo kenan kowa nakan kneel ke kina zaune to punshment ɗinki will be double." Iho ta saka "Malam dan Allah kayi hakuri wlhy na rantse ban zaunaba harna rantse Malam." Yanda Candy ke rantse-rantse taso bawa Malam Muh'd dariya amma sai ya gintse. Aga bulalan yayi ya zabga mata sau ɗaya ta mike tsaye tana rokonsa da kyar ya bula'leta sau ukku. "Mugu kawai haka zaka kare", Sannan ta wuce aji tana harare-harare kowa a ajin sanda ya nutsu.
```BAYAN SATI BIYU```
Da dare Candy na kwance tun safe yau basuyi waya da Mr smiles ɗinta ba duk sai taji babu daɗi. Da misalin takwas da rabi taji rurin wayanta kamar bazata ɗauka ba ammah sai tayi tunanin shine. Tana ɗagawa kuwa sai sunansa ta gani bayyane jikin screen ɗin rangaɗa'ɗau. Wani lallausa murmushi ya baiyana akyak'kyawan fuskanta. "Hi handsome! Av'been waitin for ur call since morning,hope all is well with u"? Shiru taji bai ansa taba sai can taji yace "kiyi hakuri dan Allah yau ina cikin tashin hankali mara misaltuwa" mikewa tayi daga kan gadon "OMG meke faruwa haka?wani abune yasameka?" Ta jero masa waɗannan tambayoyi. "mum ɗina ce ta rasu ɗazu da asuba." "Innalillahi-wa'inna-ilaihi raju'un" candy ta furta tareda dafe kirji. (0o ikon Allah yau Candy ce da jajanta mutuwa) "meya sameta ko dama batada lafia ne"? "lafianta lau wlhy,ɗazu da safe taketa complaining ciwon kai,sai tasha magani daga can shikenan bata tashi ba." Candy ta zaro ido hankali tashe dan mutuwan ya tsorata'ta. Ahankali ta furta "Allah ya rahamsheta yasa ta huta" muka haɗa baki wajen faɗin {"first in history."} "ki sanar da mama dan Allah jibi sadakan ukku zanzo sai muje ki gaishesu," "to shikenan zan sanar da ita Allah kara hakuri." "Ameen" yace tareda katse wayan.
```WASHE GARI```
Candy na kwance aɗaki tana game da wayanta sun gama waya kenan da Abdoul. Taji an faɗo ɗakin pamm kamar an wurgota har Candy ta tsorata ta yasar da wayan tana neman hanyan ɓuya. "mustew ammah miemie-bee ni bansan ke wace irin sokuwa bace wallahi,bakisan irin haka zai iya saka mutun cikin wani hali bako,yanzu da hawan jini gareni da na mutu." bee batayi magana ba ta sanu waje daga gefen Candy ta zauna tareda dafata "kawata yau ko zagina kikayi bazai dameni ba,dan nazo miki da daɗa'ɗan labari" candy ta tashi zaune tace " ke dan Allah"? "Eƴƴ mana ba har zagina kike ba, wani yasuwa akayi anguwan mu, Kinga kuɗi kawata wallahi masu kuɗine na hakika kinga ruwan juice da kaji da ake goge hakora da wanke makoshi. "mustew shine kike son kasheni sabida ɗan wannan"? Toh bazani ba dallah ki kyaleni ina cikin jimamin mamar mijinda zan aura ta rasu." wangale baki miemie-bee tayi cikeda mamaki Candy gidan *Zaman makoki* nefa" "ke ba gidan zaman makokiba ko inane bani zuwa ayau" da kyar dai bee ta zuga Candy zuwa gidan makokin da aƙe. wannan shine karo na farko da Candy taji bataso zuwa gidan zaman makoki ba. Gidan su Munay suka je tare da sanar mata komai cike da murna ta zaro hijab suka fita.
Suka kama hanya sai kofan gidan suka bi mutanen da ke ta shiga gidan suna shiga cikin gidan Candy tayi mutuwar tsaye dan yanda taga gidan tsaruwa iya tsaruwa ya tsaru wanda yasata sakin baki tana kallon gidan. Cikin gidan suka nufa nan ne suka sake ganin haɗuwan gidan ammah kowa kuka gani cikin gidan yana cikin bakin cikin rabuwa da mamacin. Abinci aka kawo ga paper soup, gasasshen nama,da kuma drinks ammah babu wanda yayi masa kallo biyu. Su candy sai zazzare idanu akeyi matan tace "bismillah mana" tana nufin su sami wajen zama dan gaida yan uwan mamaci. Ammah ina su a'tsammaninsu ancene suci abincin, habawa suka rufu akan abincin kamar ba gobe basu lura da irin kallonda ake musuba.
Wata yar budurwace ta shigo ganin su Candy kasa magana tayi ta tsaya tana ganin ikon Allah.
Candy ci take ba sassauci ganin cikinta yasoma dauka sai ta zaro wasu laidan Walima kwaya biyu ta soma juye abincin aciki dai-dai nan wata mata suka shigo da gani kamanin su dayane ko muce ma yarsa ce, tare da *Abdul-wahab* suka shigo dakin cikin razana Candy ta dago ga laida ta shake shi da shinkafa da nama. Turus *Abdul-wahab* suka tsaya. "Yasalam" Candy ta ce take yayan hancin cikinta suka soma juyasa shikenan yau mai aukuwa ra auku. Abin kunya agidan *SURAKAI.*
*TAGWAYEN MARUBUTA*
0 comments:
Post a Comment