New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 61-70

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧

                           *NA*

*Rash kardam*
         *Ummieluff* 

Page
*61to70*         

Jan k'afarta take yi har ta iso k'ofan gida. Sai da ta tsaya k'ofar tana tunani shiga don yanda take jan k'afar. Ta kai minti goma a gun kafin ta shiga cikin gidan da sallamanta.

Umma da ke fama da itace a murhu sai hayaki yake yi idonta duk ya kaɗa yayi ja-jazur. Ta joyo tana fifita wuta ta amsa sallaman Candy ganin k'afarta na ɗin gishi, da sauri Umma ta yarda abun fifita, ta nufo gunta ta na ce wa"lafiya Candy mai ya faru dake naga k'afarki na ɗingishi?".

Idon Candy ya ciko da kwalla Umma ta ce"ki faɗa min mana Candy duk hankalina ya tashi".

Hawayen da Candy ke mak'alewa ya zubo, cikin muryan kuka ta ce"Umma ba Malam Muh'd bane don yaga muna faɗa da Rabeer'at ya dake ni, kuma ita ce da niman tsokana".

Umma ta ce"kai amma Allah yayi ma Muh'd ɗinnan albarka da ko zan ganshi da na gode masa".

Candy ta zunɓuro baki ta nufi ɗaki.

Umma ruwan zafi ta juye ma Candy ta kai mata bayi. Ta je ɗakin ta ce"ki je ki watsa ruwan zafi zaki ji daɗin jikinki".

Candy ta mike da kyar ta nufi bayi ruwan da zafi haka ta ringa watsawa tana faɗin "washh!!. Sai ta yarfe hannuta sabida zafi. Tana gama wankan ta ɗauro zani ta fito sai taji daɗin jikinta, man zafin da ummah ta ajiye matane,ta shafe dukkan jikinta dashi,sannan ta ɗan samu sa'ida, tayi sallah taci abinci ta sha maganin ciwon jiki,ta kwanta barci mai nauyi ne ya ɗauketa.

Candy bata farka ba sai bayan sallah la'asar, ta tashi tayi sallah ta ɗanji daɗin jikinta. Yau zama tayi ko k'ofa bata fita ba dan k'afarta yana ɗan taɓata har yanzu.

Zama tayi ta zabga ta gumi tana tunanin kalan dukan da zatayi ma Rabee'at in ta kamata.

Washe gari bata je makaranta ba sabida yanda k'afarta ke taɓata amma da sauki.

Malam Muh'd yana zaune a gindin bishiyar da yasa ba zama yana kallon wucewarta. Duk ya damu yanda yaga 'yan latti nata wucewa babu alamanta wani karin abun haushi kusan k'arfe tara ba labarinta. Duk sai yaji zaman Makaranta ya ishesa. A can k'asar zuciyansa kuma cewa ya ke"gaskiya nima ban kyauta ba hukuncin dana bama Candy yayi tsauri inaga hala k'afarta ne ya da meta".

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaɗaga kai ya ga har an rufe gate ɗin makaranta. Jiki ba kwari ya mike ya nufi office, yana mai jin haushin kansa sosai akan hukuncin da ya mata.

A cikin aji Mamu da Kausar Lurv suna zaune jigum Mamu ta ce"Kausar ki ga har 9:00 yayi Candy bata zo ba ko lafiya".

"Hmm". Mamu ta sauke ajiyar zuciya ta ce"nima Kausar tun ɗazu nake tunani anya ba k'afarta bane ya dame ta?". Kausar ta ce"in kuma ta wahala Mamu sai mun daka Rabee'at don ita ce silla, sabida kinga  asali gurin zaman Candy ne ta zauna, shi kuma wannan mugun Malami ya dake ta".

Mamu ta ce"nifa yanzu haushi yake ban ya wani saka mana ido baran  Candy ma kusan kulum sai ya bata punishment".

Kausar ta ce"ke dai bari kawai in an tashi zamu bi gidansu mu gani".

Malam Muh'd ya tsinci kansa cikin nadaman abunda ya mata da wannan tunanin har aka tashi daga makaranta. Jiki ba kwari ya nufi gida abunsa.

Mamu da Kausar suka bi gidan su Candy nan suka samu k'afar yayi sauki, ta kuma shaida musu gobe tana zuwa makaranta.

Sallama suka mata suka tafi gida.

Washe gari Candy ta tafi makaranta cikin shirin kota kwana  don sai ta rama abunda aka mata akan Rabeen Gwaggo....lol..

Malam Muh'd ganin Candy yau yaji sanyi a ransa. Bakar gilashinsa ya mannata wanda ke kara masa kyau, hakan kuma yake basa daman kare ma Candy kallo. Yarinyan tana burgesa gata da k'ok'ari sai dai bataji abunda ke haɗa su da ita kenan kuma baya sake mata.

Aji suka shiga akayi ka nan suka zauna ana musu karatu sam Candy bata nuna ma Rabee'atu Gwaggo komai ba. Hakan yasa su Rabee da kwayenta sai dariya da zunɗe suke ma Candy.

Ana tashi Candy ta ja su Mamu suka laɓe a wani gida suna kallon su Rabee sun ɗau hanyan gida suna dariyan mugunta akan dukan da akayi ma Candy suna dariya suna faɗa. Sai da suka shiga lungu Candy ta fito da sauri su Mamu ma suka biyo bayanta tana zuwa ta sha gabansu take ido ya raina fata. Rabee tana shirin artawa da gudu Candy ta cafko ta ta haɗa ta da bango nan ta fara jibgarta kamar ta samu jaka. Sai da ta lallasata su Mamu kuma sukaji da yan koren Rabee. Su Rabee sai hawaye, Candy ta ce"saura naji kun sanar da wani ko ya je kunnen Malam Muh'd hahaha!!". Tasaki dariyan mugunta kai ta gir-giza musu alamar kun san sauran.

     _*```TAGWAYEN MARUBUTA```*_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts