🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI* 🍧🍹
```Ummieelurv😘```
&
```Rashida A Kardam```
Page➖121-130
Kasa magana Abdoul yayi dan besan me zai ce ba shi da kansa kunyan yan uwansa ya kamashi he'iz speechless ammah kina ganin idanunsa kinsan akwai matsala dan ransa yayi mutukar ɓaci da abunda Candy tayi masa. Shin wannnan wace irin macece?
Shin mema yakaishi neman yarinya irin Candy?
Shin meyasa bai yi bincike ba kawai ya afka soyayyah da ita?
Shin me yan uwansa zasu ɗauke sa?
Mutuminda bai san abunda yake yi ba mana. Wani zuciya ya sanar dashi. Kallon Candy yake da disappointment a kwayan idanunsa. Baiwar Allah kuma jikinta yayi sanyi sosai wanda bata taɓa tsammanin akwai rana irinta yau da abu irin haka zai sameta ba. Wayyo Allah nashiga ukku. Yanzu yaya soyayyanmu zai kasance?
Anya kuwa Abdoul wahab zai yarda da aurena ayanzu?
Anyan yan uwansa zasu sake yarda dani kuwa? Innalillahi-inna'ilaihi Raju'un ya Allah ina neman mafita agarwka.
Da kyar Abdoul wahab ya buɗi baki yace "Yanzu Khadija abunda kika yimin kin kyauta kenan? Yaya za'ayi kizo gidanmu ki zubda min mutunci ki kuma zubdawa kanki mutunci,wane irin rayuwane kika sawa kanki? Kina ganin abin burgewa ne kizu gidan makoki kike cin abinci kina nishaɗi,bakya tunanin kema wata rana naki zai iya rasuwa azo gidanku amiki irin abinda kika min yaya zakiji kenan?". Ee'e nasan bai kamata azo gidan makoki ayita ihu da koke'koke marasa amfaniba,hasalima anfison ku zauna daga gefen wacce akayiwa rasuwan kuke ɗan hira dan yaɗan rage mata kunci da takeji agame da rashin da akayi mata. Ammah kirasa abunda zai saki nishaɗi sai zuwa gidan makoki bama dan jajanta musuba a'a ke kawai dan kice abu mai daɗi. Baki damu dame yan uwan mamacin zasu jiba ganim suna bakin ciki,keko kina farin ciki.
Kiduba wannan mahaifiyata ce tarasu duk da naji zafin rasuwan'ta ammah abinda kika min yafi yimin zafi dan kin nuna baki damu da damuwana ba, ya nuna bakya *tare'da ni* kenan,mahaifiya tace ba taki ba, haka Khadija abunda zaki saka min dashi kena? Duk irin tsananin so da kauna dana nuna miki,na kudiri niyar mayar dake u'war ya'yana,ashe Allah yataimake ni daban aureki ba kika haifamin yara masu irin halayenki, Kaichona." banda kuka babu abinda Candy take Arayuwa bata taɓa soyayya ba sai akan Abdoul,bayan Ummanta babu wanda take jinshi har'a zuciyanta irinshi. Abdoul shi kaɗai nakeso banajin zan'iya kaunan wani kamarshi gashi yanzu abinda yasameni kenan. Kai Allah na tuba. Mikewa tayi jiki asanya'ye ta isa garesa "Abdoul nasan nimai laifice agareka ammah ina rokonka dan Allah kayi hakuri,nayi maka alkawarin daga rana irinta yau na daina abinda nakeyi matukar ka yafe min kuma ka yarda zaka aureni wallahi harna rantse maka bansan nan gidanku bane,Abdoul ni yarinyace bansan komaiba banda sonka,dakai nasan me ake nufi da kalman so, *So ɗaya tak* nake maka dan Allah kayi hakuri." tana kaiwa nan ta fashe da kuka abun gwanin tausayi miemie-bee banda zare idanu babu abinda takeyi awajen duk abinnan dayake faruwa tana rike da ledanta data ɗura zalalan tsokan naman kaza aciki. Kuka Candy take har tsungunawa agaban Abdoul tana rokonsa daya yafe mata. Ɗagota yayi cike da so yana share mata hakaye "ki daina kuka beauty na,yaranta ke damunki na yaff-" bai karasa ba wacce muke tsammanin yayar sace tayi karap ta buge hannun Abdoul tareda fashewa da kuka "Ashe bakada hankali Abdoul,ashe zaka iya zaban soyayyah over mahaifiyarmu wacce ta kawomu duniya." kuka take harda majina ita adole batason Candy "idan har kana sonta to saida kazaɓa ko mu ko ita-" "a'a haba ya'ya ki daina wannan zancen dan Allah yaya ma zaki soma faɗin irin waɗan'nan muna'nan kalaman." wani kallo yawatsawa Candy "tashi kije nagode kema wata rana zakiji irin yanda naji nima" kuka take tana rokonsa ammah yaki sauraronta badan ranshi nasoba yakori Candy koran kare daga gidansu idanunsa sun rine jajaye.
"a'a dawo mana ki ɗauki ledanki wazaki barmawa"? Candy ko kallon inda Yake batayi ba wannan shine karo na farko da Candy ke ganin kaza da idanunta ammah ta barshi bataci kota sace ba. "kee zoki ɗauka mata" sukace da mie-mie ko kunya babu ta juya zata koma wani irin shaka Candy tayi mata ta rinka janta kamar tinkiya har suka fice zuwa bakin gate. Suna fita tayi wulli da ita tareda watsa mata kyawawan mari guda 2" Ammah dai miemie-bee Allah ya isa tsakanina dake,har duniya ta naɗe bazan yafe mikiba,sanda nace miki bazan zoba kika nace sanda nazo yanzu me kika janyo min kenan"? Miemie dake kuka tace "wallahi candy kiyi haKuri bansan haka abun zai kasanceba." 'dan uwarki da kika sanin ma kin mutunta nine inace komawa kikayi niyyanyi dan ɗauko min leda,wallahi kika sake magana zan ɓabɓallaki munafuka kawai." miemie zatayi magana candy ta ɗaga hannu kamar zata mareta ta gudu.
Kuka take ta shiga gida yanda umma taga idanunta da yanda take kuka yasata rikicewa "ƙhadija meya sameki kike irin wannan kuka haka"? candy babu ansa sai kuka tanason ta faɗa mata tana tsoro "ummah mamar kawata ce ta rasu shiyasa nake kuka" "aiya addu'a yakamata kiyi ba kuka ba kirinks mata addu'a, dafatan dai bakiyi halinkin a gidan zaman makokin ba"?zaro idanu tayi cike da tsoro kamar umma ta ganota. Da haka dai tarinka lallashinta ranan ai candy batayi bacciba,tana rufe idanunta photon abinda yafaru take gani adanunta. Tashi tayi ta zauna tana jimamin rabuwa da mr smiles ɗinta.
****
Tun daga wannan ranan Abdoul bai sake bi ta kanta ba. Don yan uwansa sun rabasa da ita. A haka har akayi bakwai ya koma bakin aikinsa.
****
Candy duk ta rame ga yawan tunani Umma tayi faɗan har ta gaji sai addu'a take mata. Candy kulum cikin zuba ido take ko Abdoul zai dawo shiru.in takira wayansa baya ɗauka, daga karshe ma yayi blocking ɗinta. Wani sa'in taci kuka a ɗaki ita kaɗai duk damuwan duniya ya isheta. Saukin da ta sami yanzu sam Malam Muh'd baya shiga sabgarta. Ya rage tsangwanta..
****
*BAYAN WATA BIYAR...*
Haka rayuwan Candy ya ci gaba da tafiya ga Ummanta yanzu bata da ishashen lafiya yanzu wataran ita ke wankin kuɗin, don ta sama musu abunda zasu ci dana maganin Ummanta. Kullum cikin kuka take da rokon Allah ƴya tashi kafaɗun Ummata ya bata lafiya.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
0 comments:
Post a Comment