New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MAI SANDA PAGE 7

: HANNUNKA MAI SANDA.............

Sanah S Matazu

Rash Kardam

7

A ranar Aunty Halima ta koma ?akin mijinta,cike da godiyar ubangiji da ya azurtata da miji salihi managarci mai hakuri.Fani ?aya kuma tana godiya ga ubangijin daya bata kishiya mara kyashi da hassada tas Murjanatu ta zauna ta zayyane mata yadda ta dinga kulawa da hidimarsu sossai taga sauyin ?abi'a tare da yaranta musamman Muttaka.
Kamar kodayaushe zaune suke suna hira cike da nisha?i Malam Auwal ya shigo nan da nan yaran suka mike kowa kokarin nuna masa kulawa yake wani da?i ya kwaranya a zuciyarsa can ya sauke idonsa kan Muttaka daketa kumburi kamar kwa?o.
"Ya aka yi yaron Abbansa?".
Turo baki ya yi yana gunguni,

"Abba wai Mama ce ta ce nayi kankanta da yin azumin da zasu fara gobe har zuwa ranar arfa.Kawai ladane basa so in damu ko Abba?".
Murmushi ya yi kannan ya ce,
"ai ko kayi Auntynka za a bawa ladan bakai ba".
"Zanyi murna in ambaku ku duka Abba, saboda Mama ta gayamun bani da abinda zan biya Mama bisa ?awainiyarta gareni.Sannan azumin nada falala ita ce ta gayamana ?azu".

"Lallai abinma wariyar launin fata ne, to ?kuwa nima azo abani falalar inji in karu".
Murmushi suka yi gaba ?aya dai-dai lokacin ya zauna kan shimfi?ar da Murjanatu ta yi masa.Maryam ta kawo ruwa mai sani Sa'adatu ta ajiye masa abinci.Ransa fes ya dinga sa musu albarka.

Cikin murmushi ya dubi Aunty Halima,
"Auntyn yara ko dai ke zaki bani fatawar da Maman Yara tayi muku ne?".
Cikin murmushi ta sune kai, a hankali yanzu mugun nauyinsa take ji game da abinda ta yi masa a baya.

Cikin murmushi ta ce,
"bafa wani abu bane tadai kwa?aitar damu azumtar watan nada lada sossai musamman na ran arfa".
Shima cike da kulawa ya ce,

"tabbas azumin nada lada tare da matukar muhimmanci ubangiji ya bamu ikon yi amin".

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts