MOTAR KWADAYI
36-40
Bayan k'wana biyu, Khaleel ya dawo, yaro ya aika, ya kira masa Ayshat. Dai-dai lokacin Malam ya fito, yaji ana cewa a kira Ayshat, Khaleel yana ganinsa, yarusuna ya gaida shi, Malam Yace"kaine ka aika Ayshat tazo?. Khaleel ya rusuna tare da sunkuyar da kai," eh nine Baba. Malam ya kalesa sosai, yaron yana da nutsuwa, a tare da shi. Malam ya kaleshi Yace"ina fatan lafiya dai ko?. Khaleel ya k'ara rusunar da kai, "lafiyalau Baba, daman sai ya d'anyi shiru, Malam yace"ina jinka yaro, Khaleel ya sanar da Malam abunda ke tafe dashi. Malam ya ji dad'i kuma Allah ya tabbatar mana da alkairi. Bari na turo maka ita, Malam yana shiga cikin gida, d'akin Amina ya shiga, yana zama Ayshat ta gaida shi, Umma sanu da zuwa ta masa, ya amsa fiska sake, gyara zama yayi, ya kali Amina, a "hankali ya kira sunanta, ta amsa masa, nan ya fara bata hak'uri, akan abunda ke mata, murmushi tayi bakimai Malam. Nan ya fad'a mata mai son Aysha ne yazo, kuma ga dukkan alamu, yana da nutsuwa da hankali, na bashi daman yazo, su sasanta kansu, ina son kema ki cigaba da addu'a. Ta nisa "ba komai Malam Allah ya mana zabin alkairi, Umma tace"Mamana tashi kije ku gaisa, cikin jin kunya, ta d'au hijab d'inta ta fita.
A zaure ta taras da shi, da sallama ta 'karasa gurin, cikin fara'a ya amsa, sun gaisa tayi shiru, ta sunkuyar da kanta, a hankali ta d'ago, karaf suka had'a ido. Wani lallausar murmushi ya sakar mata, ita ma murmushin tayi, cikin murya mai kama da rad'a, yace"my beauty kinyi kyau sosai. Ayshat bata san lokacin, da ta murmusa har saida, dimple d'inta suka lotsa. Suna haka saiga Safiya cikin Matsatsun kaya, tana taku dai-dai, tana shigowa zaure burki ta taka, ganin Ayshat na hira, hirar ma irin ta kauyawa, wanda basu wayeba, bata san lokacin da ta fashe da dariya, har tana rike cikinta.
�Inna tana jin dariyan Safiya, ta fito da sauri, ganin abunda Safiya ke ma dariya, yasa itama tafara, Malam dake d'aki jin dariya, yaki karewa suka fito shida Umma, yana zuwa zauren ganin, abunda sukayi masu Ayshat, tsawa ya dakamusu, Inna ta masa kalon uku saura kwata, suka tafi suna dariya. Malam hak'uri ya bama Khaleel, suka koma cikin gida.
Sannu a hankali soyayya gamida sha'kuwa, suka shiga tsakanin Khaleel da Ayshat, harta kai magabata, sun shiga al'amarin, a tsayar da biki su, Aysha na kamala Secondary school, shi kuma yagama bautar kasansa sai ayi Aure.
WAYE IBRHIM KHALEEL?.
�Ibrahim Khaleel, asalin iyayensa yan Yola ne, zamane ya kawo su garin Kaduna. Su uku ne a gun iyayensu, shine Babba sai kanwarsa, Hafsat dake aure a badarawa, sai autarsu wacce bata wuce 14yrs ba, Umma Halima itace mamansu, kuma ita kad'ai Malam ya aura, bai k'ara aure ba. Malam Kabir mutum ne mai kirki, yana sana'ar sai da kayan koli, duk da rashin k'arfin da ke dashi, hakan bai hanasa tsayawa, tsayin daka gurin ganin Khaleel yayi karatu, cikin ikon Allah ko da kunbiya-kunbiya, had'a har Khaleel ya kamala karatunsa, a fanni kasuwanci, yanzu haka yana bautar kasa. A cikin garin Kaduna, Khaleel yaro ne mai farin jini da kamala, shiyasa duk inda yaje, yana da mutane, kuma yana da hak'uri sosai.
Friday, 24 February 2017
Home »
» MOTAR KWADAYI PAGE 36-40
MOTAR KWADAYI PAGE 36-40
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment