New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE 58-60

[7/5/6:47am]

🌲RASH KARDAM🌲🌲
               &
🎋SADEEY S ADAM🎋
            WITH
💖💖BEEBAH LUV💖💖

  🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
        MAYA'UDARA
     🌺🌺🌺🌺🌺🌺

                     58-60

Teemah tayi sallama wa Umma ta fito daga gida wani had'add'e mota ne ya faka a gabanta tare da zuuge glass d'in motar fiskansa d'auke da murmushi ya sakar ma Teemah. Cikin ta kun k'asaita Teemah ta iso gefen motar ta kallesa ta ce"ai na d'auka bazaka zo ba ne". Sai da yayi murmushi ya ce"hajjaju ayi hak'uri go slow na samu a hanya shiyasa". Fitowa yayi ya bud'e mata k'ofar gaban motan tashiga ciki suka bar unguwan.

Tafiya mai nisa sukayi kafin suka iso k'ofar wani makeken hotel nan ya danna hanci motarsa suna zuwa suka fito d'aki mai lamba goma suka shiga ba laifi d'akin ya mugun had'uwa bana wasa ba. Teemah suna Shiga tayi jifa da Jakarta ta cire hijab d'in dake jikinta wani riga ne mai hannu best ko cibi bai sauk'a mata ba, sai wando wanda zamu iya kiransa da shi da babu duk d'aya ne.

A hankali Nass ya tako gunta tare da janyota jikinsa nan ta fara aika mata da sak'onninsa ganin sun shagala da yawa muka bar d'akin.

Teemah basu bar hotel d'innan ba sai da magriba ta koma gida cikin ladabi in ka ganta ka d'auka Ustaziyan gasky ne hijab har k'asa ga nikaf Umma har tana alfahari da Teemah tana da nutsuwa, hankali ga kamun kai.************

3 months latter.
Teemah na hango kwance ta rame tayi bak'i bakintan nan yayi ja-jazur da shi ya d'an kwaile, Umma ne ta shigo tana fad'a "Fatima nikam nagaji kulum kina kwance a gida ga ciwo sai cinye ki yakeyi jibi fa yanda kika dawo duk ki banki kin gama ramewa". Da kyar Teema ta d'ago kai ko da muka kalleta sai da mikayi baya da sauri wannan kamar ba Teemah ba.

Kasa juran d'aga kai d'in tayi ta koma ta kwanta Umma ne ta fita ta kira mai Napep ya zo har k'ofar gida ta shiga ta d'auko Teemah da ta dawo kamar kwarangwal suka shiga Napep suka tafi Asibiti.

Suna zuwa aka basu gado nan aka d'ibi jininta da fitsarinta aka gwada gwajin farko ya nuna musu cutar k'anjamau take d'auke da shi, Likitan da kansa yazo ya samu Umma sai da ya mata nasiha kafin ya juya ya kalli Teemah cikin ta kaici da yaji budurwa ce ya ce Fatima kina s'auke da cuta mai karya garkuwan d'an Adam, take Teema ta zaro ido Umma kam yankan  jiki tayi ta fad'i a k'asa sumamiya, Teema jiki ba k'arfi ba halin mik'ewa sai dai kuka takeyi, Dr ne ya kira nurse sukazo bata taimakon gaggawa.

Cikin ikon Allah ta far-fad'o nan ta fara tuna mai ya faru kuka ta saki tana fad'in Fatima ta cucesu ta zubar musu da mutunci yaushe ta yarda tarbiyan da ta bata da wannan tunanin bacci ya sake d'aukanta.

Gidansu Areef biki ake ba sanya Walima kawai hajiya ta shirya sai dinner ranar jumma'a bayan Sallah jumma'a dubban mutane suka shaida auren Areef da Hameeda auren da ya tara manyan mutane bayan d'aurin aure maza suka wuce hotel dan gabatar da liyafa da yamma kuma akayi waliman mata, waliman da ya tara jama'a anyi wa'azi mai ratsa jiki wanda yasaka Hameeda jin zatai ma Areef biyayya koda zai wukanta ta don niman aljannata.

Da daddare angwaye suka fito cikin shirin dinner ko da na kallo Areef shima yasha kyau ana haka a ka kwashi kawaye suwa gun Hafcy na hango ta rik'o hannun Hameeda cikin wani cut less mai tsada sai kyalli takeyi ko da Areef ya hango ta sai da k'irjinsa ya bada rass!!! Cikin zuciyarsa ko cewa ya ke"tsarki ya tabbata ga ubangijin halita tabbas Hameeda tayi kyau ba na wasa ba". Kasa d'auke idonsa yayi ko mai ya tuna take yayi tsaki yana mai jin haushin kansa da irin kallon da yake mata.

               Written by
         🎋S💖B🌲R💕

  [Truncated by Whatsapp].

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts