🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧
*```Rash Kardam```*
*```Ummieluff```*
Page➖ 101-110.
Tana shiga cikin gidan ta ɓoye kuɗin cikin zaninta. "Aww harkin dawo hala gidan da nisa" "Eee" kawai ta ceda Ummah. Sannan tabi lafiyan gado lumshe idanu tayi tana kallon kayatac'cen murmushinsa wani ihu ta saki tareda rungume pillow a'hankali ta furta wannan shine ```Mr Smiles•```
Sai da ta gama tunane tunane ```Mr Smiles``` ta tashi ta cire kayan jinkinta, wani dogon riga ta dauko na bacci ta sanya tukun ta hau gado tayi addu'a ta kwanta cike da tunanin saurayinta. Washe gari ya kamata talata ranan Candy da wuri ta shiya zuwa makaranta a cikin kudin da ```Abdoul Wahab``` ya bata ta dauko dubu ɗaya da biyar ta ɓoye a cikin littafinta. Umma ta kalli Candy ta ce"yau bazaki karya bane?".
Take Candy 'yan hanjinta suka motsa. Cikin yanayin rashin kuzari ta kalli Umma ta ce"zanci amma yau cikina ke ɗan juya min kamar ya ɓaci".
Cikin alhini Umma ta ce"ashsha! Ashsha!! Sannu to ki rage ciye-ciye gudun karya kara ɓata miki ciki. Gashi ba wani kuɗi a hannuna da kin je chemist ki sayo magani. Yanzu ki ɗan shafa toka a saman cikinki zakiji dama-dama". Duk Umma ta damu akan Candy.
Candy ta ɗauko kwanon abinci taci kaɗan ta mike ta ce"Umma na tafi sai na dawo" Ta sa kai ta fita.
Tana fita ta nufi wani shagon da ke kan hanya ta sai cake da nutric milk gora uku ta bashi kuɗin ta nufi makaranta. Tana zuwa ta samu ba a wani zo ba, hakan yasa ta ciro cake ɗin taci sannan ta ajiye wa su Mamu nasu.
Ba da daɗewa ba su Mamu suka zo nan fa ta mika musu tare da basu labarin komai. Su Kausar sun matukar tayata farinciki da addu'a alkairi, a haka suka ɗau darasin ranan har aka tashi a makaranta.
A hanya taga wani karamin restaurant nan ta tsaya tai musu take away biyu na jelop rice da yaji naman saniya akai da maltina gwan-gwani hudu. Ta saka a leda ta nufo hanyan gida.
Tana zuwa k'ofar ta ja ta tsaya nan tunaninta ya dawo cikin zuciyarta ta ce"yanzu in an tambaye ince a ina na samu". Kai ta ɗaga tana nazarin abun can ta saki wani lallausar murmushi ta nufi cikin gidan da karfin gwuiwa tana zuwa kwaɗa sallamanta da karfi "Assalamu'alaikum"
Umma ta amsa mata da "Wa'alaikumusalamu". Ta na shiga kallo daya tayi ma Ummanta ta gane ba abbinci. A hankali ta zauna a tabarma tare da faɗin "washh!! Yau na gaji". Umma ta kalleta cike da kulawa ta ce"sannu ya makarantan?".
"Alhamdulilah!!". Candy ta faɗa tare da miko ma Umma laida.
Umma ta kalleta ta ce"miye aciki kike miko min?". Cikin muryan shagwaɓa Candy ta ce"Umma ki buɗe ki gani tukun".
Umma tana buɗewa taga take away cikin kallon tuhuma ta ce"ina kika samo wanan?".
Candy tayi murmushi ta ce"Ummana munje debate ne yau aka rarraba mana nikuma na ɗau har biyu nasan muna da bukata".
Umma ta ce"kinsan ba kyau haka kowa ɗaɗɗaya aka bashi ke ki ɗau ɓiyu".
"Umma ai na faɗa ma Aunty mu ni bazanci a gun ba zanzo dashi gida shiya ma na ɗau biyu kuma ta sani tace ba matsala".
Umma na jin haka ta sauke ajiyar zuciya nan suka ci abimci harda barin saura suka kora da drinks abunsu.
Haka Candy tayi ta gudanar da rayuwa cikin kwana uku sai tai dabara sun ci abinci mai kyau. Ba tare da Umma ta gane ta ba.
Yau ta kama jumma'a da yamma Candy taci kwaras ɗinta da atamfar sallanta ba laifi tayi kyau sosai. Littafin turanci ne a hannunta tana dubawa wani yaro yazo da sallama.
Candy ta ams yaron ya ce"wai ana sallama da Candy a waje".
Umma ta ce"inji waye haka?".
Yaron bai daɗe ba ya dawo ya ce"wai inji ```Abdoul wahab ne".```
Candy ta ɗan kalli Umma ta ce"kaje kace ina zuwa". Yarin yana fita, Umma ta ce"Khadija yaushe kika fara hira ban sani ba?".
Candy ta maraice fiska ta ce"Ummi na kiyi hakuri wallahi yana da hankali sosai". Nan taba ma Umma labarinsa, Umma ganin yarta Candy tana son *ABDOUL WAHAB* yasa ta aminta ta bata izinin fita tare da fatan alkairi.
Candy tana zuwa k'ofar gida ta canza salon tafiyarta tamkar wata hawainiya cikin nutsuwa da takama ta ke tafiya. *Abdoul wahab* zuba mata mayatattun idon sa yayi ya kasa ɗauke kansa daga kallonta. Cikin zuciyarsa ko cewa yake"gsky duk cikin matan zamannin banga kamar Candy ba komai nata dabanne ga aji tabbas nasan nan gaba gogewa kaɗan zatayi ta zama mace mai class, mace wuce raini, mace nuna ma sa'a".
Wani lallausan murmushi ya sakar mata dai-dai lokacin da ta karaso gurin. Cikin yanga ta kara make murya ta ce" *Mr Smiles* ka yini lafiya? Ya jumma'a?.
Abdoul wahab mutuwar tsaye yayi sabida yanda Candy ke sarrafa bakinta da sunan da ta kirashi da shi. "tabbas baki yi karya ba sunan ya dace dani kuma ya min daɗi gaskiya ni mutum ne mai yawan murmushi."
Candy tayi wani fari da ido kai ka ɗauka wata babbar macece yanda take iyaye, duk ta rikita Abdoul wahab. Cikin kan-kani lokaci suka kara sabawa hira suka yi sosai.
Sai dab Magriba Abdoul Wahab ya mata sallama tare da mika mata wasu manyan laidoji guda biyu.
Candy ta ki karɓa sai da taga ya bata rai kafin ta amsa ta masa godiya ta shiga gida.
Ko da ta shiga Umma faɗa tayi mata na karɓan kaya, nan ma tayi bayani ma Umma akan taki shi ya dage daga karshe Umma ta sanya ma abun albarka kafin suka buɗe kayan da ke ciki kamar haka; riga da skirt guda biyu dogon riga biyu sai atamfa wanda aka dinka biyu da takalma uku da poss uku sai kayan shafe-shafe. Abun dai son barka don kowani kaya Candy tasaka zai haska ta bana wasa ba. Umma taji dadi ta kara godiya da sanya masa albarka.
Candy kuma rawan kai zai karu kenan tunda ansoma yin kaya masu kyau...lol..
Bayan kwana biyu Abdoul Wahab yayi mata sayya na kayan makulashe sosai. Ya sai mata waya Samsung Galaxy.
Tun daga wanna rana suna makale da juna a waya har ya koma gun aiki.
Munay ce ta shigo cikin hanzari ta gaida Umma nan ta tambayi Candy Umma ta ce"tana daki". Ba tare da bata lokaci ba Munay ta shiga ta samu tana gyara daki tana ganinta suka rungume juna dan murna.
Munay ta ce"Candy kin kusa gama aikin ne?".
Candy ta ce"eh shara kawai zanyi shikenan".
"Ok to kiyi muje wani gida ne a kayi rayuwa can unguwan Mu'azu".
Cikin zakwadi Candy ta ce"da gaske?".
Munay ta ce" eh kai har an kai gawar ma yau kwana daya".
Candy ta ce"kai wolla har ina jin yawuna ya tsinke na kwana biyu banci abincin *Gidan rasuwa* ba".
Munay ta ce"ni ma haka".
Ba tare da bata cokaci ba ta gama aiki suka zuga ma Umma karya suka fita. Suna zuwa gidan rasuwa kamar abun arziki sukai ta kuka har sai da aka kawo musu abinci sukaci sannan suka mike suka bar gidan.
Zuciyansu dauke da farin ciki kal!! Kamar an musu albishir da gidan aljannah.
"Oh!! Muko mukace Hali a jikin rai, mai hali baya fasa halinsa a ko ina yake".
*```TAGWAYEN MARUBUTA```*
0 comments:
Post a Comment