[7/5/6:47am]
🌲RASH KARDAM🌲🌲
&
🎋SADEEY S ADAM🎋
WITH
💖💖BEEBAH LUV💖💖
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
YAUDARA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Pg0⃣2⃣
Hydar tunda ya hango ta yake smiling,ita kuwa sai gwargwasa take a hankali take tafiyar kamar mai tausayin k'asa haka dai ta k'araso gurinsa cikin kisisina irin ta mayaudaran Mata.
Jingina tayi da motar sannan tad'an had'e rai ba tare da ta kalli hydar d'in ba.
Murmushi yayi sannan ya rage glass d'in motar ya kuma bud'e Mata "Allah yasa dai banyi laifi ba",murmushin makirci tayi Wanda shikesa samarin nata su rud'e suna kallon duk duniya ba Wanda yakai teemaluf iya soyayya da kuma kyau.
"laifi ai ka gama yinsa my D kasan awowin da na d'auka ina jiranka kuwa?amma kak'i xuwa a lokacin da kace zakazo" tad'an k'ara b'ata rai "ka koma wajen wacce kake so tunda yanzu ni baka sona", a gigice ya kalleta "haba teemah kinsan kuwa duk duniya ba wacce nake so kamar ki,wlh bani da wadda ta fiki,na b'ata lkci ne wajen siyo Miki kayan da kika buk'ata pardon me pls👏🏻"
"murmushi tayi najin dad'i "dan kasan baka laifi a guna shiyasa kake min haka but next tym in ka kuma I wl punish u", bazan kuma bama" tayi dariya sannan ta Shiga cikin motar ta zauna, ya kake ya mummyna(mamanshi)?", lafiyanta k'alau tace a gaida surukarta kuma Yana son ganinki yaushe zakije mata?" , hmmm "zan duba ko da week-end ne Sai naje kasan yanzu Ina busy ga bikin bestyna ga kuma skul", ok Allah kaimu" "Ameen my D".
Sunyi hira sosai yasha kisisina da iyayyi da shagwab'a shi kuma hakan ke burgesa ga teemah
Ta wankensa sosai d'an kuwa Sai da ya rubuta mata cheque na 50k sannan ya mik'o mata Manya manyan leda guda 2 sukayi sallama ta fito daga motar sannan ta juyo ta kalleshi
"Am vry proud of u my D,Allah barmu tare har k'arshen rayuwarmu", "Ameen teemah" ya amsa a tak'aice.
"to ni zan shiga gida sbda magrib tayi ya kamata muje muyi sallah ko?" murmushi kawai yayi baya gajiya dajin zazzak'ar muryar teemah da kallon kyakkyawar fuskarta"(hmmm mukuwa SBR cewa mukai "kallon kitse akewa rogo ")
"My D ya kayi shiru?", hmmm "nothing", hmm badai zaka fad'a ba nizan shiga gida my regards 2 mumcyna"Tana Gama fad'a ta shige gida, yad'an jima dan har Saida yaji an fara Kiran sallah sannan ya ja motarsa ya tafi cike da kewar teemahluff d'insa.
********
Misalin k'arfe 02:30am Areef ne keta juyi kan makeken gadonsa ya rasa me keyi masa dad'i anya kuwa teemah unguwa taje? Ya tambayi kansa
To kodai bata da lafiya ne shiyasa tak'i d'aga wayar kuma basa so su tada mai hankali suka k'i fad'amai gaskiya da yaje?, amma yasan teemansa bata tab'a k'in d'aga wayarsa ba saidai in Bata gurin ko a silent ta saka wayar kuma data ga missed call d'insa take kiransa
Gskya ba lafiya ba dole gobe na koma gidan dan ganin meke faruwa Allah yasa dai lafiya duk a zuciyarsa yake tunanin
Tashi yayi ya Shiga toilet ya d'auro Alwallah yayi ta jero nafiloli tare da yiwa teemansa addu'a,sai da yayi sallar subhi sannan bacci mai nauyi ya d'aukeshi.
********** Tun k'arfe 11:00am teemah tayiwa bestynta waya tace dan Allah tazo yanzu2 akwai Magana
Futha na break fast taji Kiran bestynta dan haka ko gamawa batayi ba taje ta watso ruwa,tayi sauri tad'anyi makeup taja hijab tace wa mamanta tayi gidansu teemah yanzu zata dawo
"Karki dad'e Futha saboda d'aura abincin rana", "insha Allahu baxan dad'e ba" ta fad'a tare dayin waje har tuntub'e take don son zuwa taji gulma dan kuwa tunda taji teemah tayi Mata Kiran sassafe tasan da Magana.
Tana Shiga gidan teemah taja Futha d'aki ta d'ebo ledojin ta juye a gabanta,atamfofi guda 4 da Swiss lace guda 3 sai veils da kayan makeup da kuma turaruka masu sanyin k'amshi
Futha ta saki baki tana kallon kayan cike da mamaki tace "kina cutar Areef da yawa teemah ko wlh kiji tsoron Allah bafa sonshi kike ba amma kike Yi masa muguwar YAUDARA ina tausayinki Randa Allah ya tashi kamaki"
Hmmm "ya tashi kama mu dai kema ai kina YAUDARAr samarin,samarinki nawa, dariya Futha tayi sannan tace "dama in kanayin Abu sai kayi tunanin kowa ma nayi to wlh k'arya kike min besty Samarina biyu kacal kuma in kinga sun yimin kyauta su suka Sa kansu ni bana YAUDARA Kawai dai duk Wanda Allah ya zab'amin a cikinsu zan aura"
"sai kiyi tayi kuma in fad'a Miki yanxu duniya ta canza ni samarina basa k'irguwa uncountable ne wasu ban sansu ba sai recharge card ake watso min,Areef kuma tuni na gama yayinsa na wankesa sosai na yadda shi, yanxu wani hydar ne on top,in fad'a Miki bayan kayannan har cheque ya rubuta min na 50k kuma da sunanki na wankesa nace bikin bestyna za'ayi,futha wayake tausayin maza yanxu ca6 wlh wankar banxaye zanyi
dariya Futha tayi "ba dama teemah yanxu dai a karb'o kud'in a bani kaso na tunda da sunana aka wankesa", "kinma Isa keda kikace ina YAUDARAr samari to bazan bada ba" "wlh dole na fad'a Miki gskya besty ko xaki mutu,kuma sai kin bani Swiss d'aya da 5k"
Dariya sukayi su duka teemah tace "kin manta sunana TEEMAHLUFF tun muna sec skul kuka samin sunan shiyasa LUV d'in ya bini har girmana dashi na samu damar wankar samari"
"hakane kam k'awata nima dazan samu damar wanka da na wanka saboda ba kyaune dake ba makeup ke taimakonki ni kuma ga kyau ga makeup but ban iya YAUDARA ba amma nima zan Maida sunana FUTHA LURV dan na d'an wankesu kad'an ba kamar naki ba".
dariya sukai sosai teemah tace "Ashe kema kinason wankar samarin dama ce baki samu ba" futha tayi dariya sosai sannan tace " am joking fa wlh ban tab'a Jin son inyi yaudara ba" teemah tace "ohh kenan ni mayaudariya ce?", "oho Miki" suka sake yin dariya sannan suka ci gaba da hirarsu.
Urs...🎋S 💖B 🌲R
(Triple Writer's)
[[truncated by WhatsApp]
0 comments:
Post a Comment