New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE 40-45

[11/7/10:00pm.]

💖BEEBAHLUV 💖💖
             &
🌲RASH KARDAM 🌲🌲
           WITH
🎋SADEEY S ADAM 🎋

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
       MA'YAUDARAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
               40~45

         Maza tashi kaima farouk kaje ka kwanta gobe da safe mayi maganar, yace toh Allah ya kaimu mum...

           Washe gari da safe bayan sun tashi daga barchi sai da sukayi wanka gaba dayan su, sannan suka hallara a parlour, sukayi breakfast sannan mum tayi gyaran murya tace Rufaidah jiya munyi maki maganan maida ke gidan ku, amman kin nuna mana baki son komawa, ko me ye dalili?

        Rufaida ta share hawayen ta, tace mum hakane bana son komawa gidan mu, wato gidan yayata aunty farha..

   LABARIN RUFAIDAH

          Ni Rufaidah YA ce ga Alh Macciddo Gwani, aunty farha itace babbar mu, sai ni sai kuma kanne na guda biyu wanda duk tare Allah yayi masu rasuwa,, mu hudu ne kawai a gurin baban mu, nida kanwata ihsan dakin mu daya, sai aunty farha da aisha suma dakin su daya.

         Mun taso cikin gata da kulawa da tarbiyya, daidai gwargwado mahaifinmu yana kokarin Kula damu kuma babu wani kishi tsakanin mamana da kishiyarta, don kuwa in ba gaya maka akai ba babu wanda zaice kishiya da kishiya ne. Komai namu abun sha'awa.
        Anyi auran aunty farha tun ina da shekaru 5 a dunia wanda yanzu maganar da nike maku ita ma tana da yaya uku, ta farkon shekarunta 15 don kuwa me garin jiki ce ta fini girma sosai, sai kannenta guda biyu..
   
         Bayan rasuwar su baba ne na koma hannunta, farkon komawa ta gidanta lfy kalau nike zaune, da ita sai yanzu ne take nuna mun banbanci tsakanina da yayanta,, bata kauna ta ko kadan.

           Akwai wata kawarta da take zugata, kuma duk ta handame kudin da baba ya bari komai yana wurinta.

       Dalilina na barin gidan kuwa tace ta gaji da ciyar dani, da wahala dani, sai dai in ringa zuwa ina nemo mata kudi, idan saurayi yace yana sona ko ba na gari bane tace sai na kula shi na nemo kudi na kawo mata kota halin kaka,, kuma ni kadai take sawa a harkar banzar banda ciyar ta ihsan,,, tasha kawo mun maza har gida wai sai na kula su zasu bata kudi.
  
       In naki yi sai tayi ta duka na kamar jaka,, kwanaki har sai da ta turani na fadi na karya hannu,,, yanzu kuma ranar da ya farouk ya ganni ya bige ni,, wani saurayi ne dan iska, ya ganni ta aikeni shine ya biyoni har gida, naki kulashi ashe ta gan shi taga me kudi ne,, shine suka hada baki dashi ya daukeni muje unguwa, da naki binshi shine tayi mun dukan tsiya har taji mun ciwo a kafa..

          Shine ta koro ni wai tunda naki binshi in fita duk inda zanje in nemo mata kudi inje, kar in dawo mata gida sai da kudi,, ko kwana nawa zanyi inje inyi,, wayar ma ta kwace wai ai ita ta sai mun, inna nemo kudin sai a siya mun da ita.

          Wannan shine silar fitowa ta gida, ni kuma nayi alkawarin da in shiga hanyar banza na ringa kawo mata kudi na gwammace nabar gidan, don Allah mum karku maida ni gidan ku barni in tafi wani wurin,,  nayi rashin iyaye Allah ka shiga cikin al'amurana, ka bani ikon cinye jarabawar ka agareni,, ta kare maganar da kuka me tsuma rai.

       Kowa a gurin ya tausaya mata sosai mum harda kwallarta, kiyi hakuri Rufaidah insha Allahu ba zaki tozarta ba zamu rike ki, anan har Allah ya kawo miki mijin aure nagari, ba zamu barki ki tafi ba kici gaba da addua kinji ta rungume ta tana rarrashinta duk abinda su hidaya zasuyi a gidan nan kema kiyi shi kamar yadda zakiyi a gidan ku, kinji, gyada kai kawai tayi tana kuka...
    
        Farouk kam ya tausaya mata, sai dai kuma a wani bangare na zuciyar shi yana tunanin kodai karya take, amman yaci alwashin zuwa har gidan aunty farhan,
        Akwai ta yanda zai bullo mata zai gane in Rufaidah dagaske take ko karya take yadai bar abin cikin ransa har sai ranar da ya gama binciken sa.

        Ya tambayeta address din aunty farhan tayi mashi kwatance kuma ya gane. Nan dai sukai ta hira har lokacin sallah yayi...

   
            Urs.....
    🎋S💖B🌲R
    
             MUNAI MAKU BARKA DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMIN...

[Truncated by WhatsApp]

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts