[16/7/8:47am]
🌲RASH KARDAM🌲🌲
&
🎋SADEEY S ADAM🎋
WITH
💖💖BEEBAH LUV💖💖
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
MAYAUDARA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
45~50
Farouk kam ya tausaya mata, sai dai kuma a wani bangare na zuciyar shi yana tunanin kodai karya take, amman yaci alwashin zuwa har gidan aunty farhan,
Akwai ta yanda zai bullo mata zai gane in Rufaidah dagaske take ko karya take yadai bar abin cikin ransa har sai ranar da ya gama binciken sa.
Ya tambayeta address din aunty farhan tayi mashi kwatance kuma ya gane. Nan dai sukai ta hira har lokacin sallah yayi...
Bayan kwana biyu Rufaida ta sake ta saba da su kuma suma suna jin dad'in zama da ita, gata da hankali da nutsuwa hatta Mum ta yaba da hankalinta don tasan kimar babba kuma bata barin Mum tayi aiki zata karba ta taya ta gyaran d'akin Mum duk Rufaida keyi Mum ta hanata amma fir taki hakan zatayi ko masu aiki keyin aiki sai taje ta tayasu kasancewar ta saba da aiki a gun Aunty Farhat don ita ke mata komai ta mai data kamar jaka.
Farouk da kansa ya bi didigin gidansu Rufaida sai da yayi bincike komai, a binciken ma har yasamu labarin muguntar da Aunty Farhat ke mata Rufaida ta b'oye wasu ya jin-jina al'amarin sosai har sai da yaji ransa ya b'aci idanunsa sun kad'a sunyi ja.
Farouk ko da ya dawo gida sai da ya sanar da Mum d'insu tun daga lokacin komai suka d'au aniyar k'ara riketa bisa gaskiya da amana, Mum ta ce" Farouk ka bin ciko makaranta mai kyau za'a sata taci gaba da karatunta na boko dana islamiya".
Farouk ya masa ma Mum da"to nima ina son hakan zaifi zamanta a gida. Ya nafita ya tafi kasuwa ya sayomata kayayaki masu kyau nasawa da takalma kala 3 Mum taji dad'in hakan ita, ta kira Rufaida ta bata itama tayi godiya sosai.
Teema ko bata bar gidan Khaleed ba sai da ta sake bada kanta masa da ta tashi tafiya da yamma kusan magriba sai da ya biya da ita Super market ya mata sayya tukun ya sake d'eban kud'i wanda shima bai san nawa bane ya bata ya ce"Baby na sai yaushe zamu sake had'uwa don kinsan ni nakine ke kad'ai bazan had'aki da kowata mace ba, shiyasa ban so mujima bamuga junaba ina son jinki kusadani". Fari tayi da ido kafin ta ce"nima ina ji da kai bana so muyi nisa da juna kuma bazamu jima bamuga juna ba". Da irin wanna kalan sukayi sallama ta shiga gida.
Sai da ta leka taga umman su bata tsakar gida tashiga sabida karta gane wani abu ya sameta.
Teema tun daga wannan lokaci tabi ayarin 'Yan matan zamani tadawo na kowa yanzu harka takeyi da maza in har su basu nimeta ba ita sai ta nemesu,(Allah ka shirya mu da 'Yan uwan mu ka tsare mu da aikata munanan abubuwa, don zina bashine zina fitane Allah ka tsare mu).
Areef abin duniya ya cun kushe masa don ya nimi wayar Teema taki shiga ko ya shiga ma bata d'agawa yayi sirtiri a gidansu yafi a k'irga ga wa'adin Hajiyarsa gobe zai cika, duk ya rame ya fita hayyacinsa ko bancin kirki baya samu yayi.
Washe gari Hajiya ta kira Hafcy ta ce"maza kije side d'in Yayanku ki kiran min shi jikina sanyaye ta nufi side d'in don tana mungun tsoro Ya Areef. Da sallama ta tura k'ofar falon shiru bayanan sai da ta d'aga muryanta tayi Sallama ya na kwance ruf-da-ciki ya lumshe idanunsa yana cikin duniyar tunani yaji kira sai da yayi tsaki mai k'arfin kafin ya mik'e don yana tunanin Teemansa ce bai so katsewa ba.
A harzuk'e ya fito Hafcy na ganinsa jikinta ya soma b'ari cikin sarkewan murya ta ce" Ya Areef wai kazo inji Hajiya".
Dam gabansa ya fad'i don ya san kiran sai da ya d'ibi mintuna kafin ya ce"ki je ki ce ina zuwa". A da sauri tafita don yanayin da yake ciki ya bata tsoro.
Jiki ba kwari ya nugi gun Hajiya a falo ya tararta sai da ya gaidata ta amsa ya sunkuyar da kansa Hajiya ta ce" Areef ya fa wa'a din dana na baka ya cika bancika ba shiyasa na aika a kira ka". Cikin firgici ya d'ago da rinanun idonsa wanda k'ad'an ya rage su subda hawaye.
Urs.....
🎋S💖B🌲R💕
[Truncated by WhatsApp]
0 comments:
Post a Comment