New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE-16-20

[21/5/.5:19PM] 
🌲RASH KARDAM🌲🌲
               &
🎋SADEEY S ADAM🎋
            WITH
💖💖BEEBAH LUV💖💖

  🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
        YAUDARA
     🌺🌺🌺🌺🌺🌺

1⃣6⃣➡2⃣0⃣

Cikin sanyin murya irin Nata, ta amsa da"to Mum. Ta tako cikin nutsuwa ta zauna kusa da Hafsy.uban gayyan Areef, sai hararanta yakeyi, kasa-kasa yakeyi, don tunda akace za'a had'asu baya qaunar su zauna inwa d'aya, itako gata da tsoro kamar farar kura.

Mum tayi gyaran murya, cikin natsuwa da kasaita, irin na matan da suka isa, masu jida kansu. Ta fara magana"da yimusu nassiha gameda rayuwa harta gan-garo kan zumunci, ta d'anyi shiru, sanna ta kalli inda Areef yake, ya wani sha kamshi, kamar wanda aka aiko masa, da sakon mutuwa. A hankali ta kira sunan sa, sai da k'irjinsa ya bada sautin rass!  A hankai ya d'ago kai tare da amsawa, "na'am Mum".

Mum ta kira sunan Hameeda, itama ta amsa cikin nutsuwa, Mum tacigaba da cewa" ba dan komai yasa na tara ku anan ba, sai dan maganan da namuku kwana biyu dasuka wuce. Areef kaine babba, don haka na baku nan da sati biyi ku dai-daita tsakanin ku, don mun gama yanke hukunci, a kanku nan da wata za'ayi bikinku.

Cikin firgici Hameeda ta d'ago, bakinta har wani rawa yakeyi, don sam bata tsamaci za'a ce maganan Auren su bane.tana so tayi magana amma bakinta ya kasa furtawa, cikin zuciyarta,tace" wai shin ko Mum sun manta yanda ya Areef ya tsaneni ne?.
"Baya son ganina bare farin cikina.
"Ta yaya zaman mu zai yuwu?.
" nidai na san gawata suke son gani, muryan Areef ne yadawo da ita, daga duniyan tunanin da ta luka.

Cikin muryan tausayi, da damuwa Areef yace"Mum bana ki bin umarni kubane, a'a kinsani Mum ina da wacce nakeso, itama tana sona, "Mum Teemah nah! Ta nada hankali itama, gata a waye take Mum ki gane, pls ku barni na auri Teemah itace farin cikina.

Cikin bacin rai Mum"tadaka masa tsawa, eh! Lalle tabbas yau zaka gwadan kai d'an yau ne ko?. Har kana da bakin fad'an ta waye. Meye makusa a jikin Hameeda tafi Teemah nesa ba kusa ba, yarinda ban gama yarda da kamun kanta ba.

"Mum Tee.....

"Shut up! Your mouth"  tafad'a cikin zafin rai.
"Ina Teemah kace ko?.
"Areef na baka nan da 3 days matsawan ba wani feedback, to aurenka da Hameeda ba fashi.
Mum ta mike ta nufi ciki, Hafcy na ganin condition d'in yayansu, ta mike tasan yanzu sai ya huce a kanta, dakinsu  ta nufa.

Hameeda ta mike da sauri zata wuce yayi saurin shan gabanta, yanda idonsa ya canza kala, ya juya tamkar namijin zaki. Take wani tsoronsa ya dira a zuciyarsa, fitsari tafara ji, sai da matso daf da ita, runtse ido tayi don jiran saukar mari, sai taji ya shako rigarta, ido ta zaro nan take hawayeta, ya k'ara zuba kamar fanfo. Nuna ta yayi da d'an yatsa, Yace"kee wallahi wallahi kinji na rantse ko matsawan kika sake kika yarda aka had'a auren nan sai na lahira ya fiki jin dad'i. Don bana sonki baki cikin tsarin matan dana keso, mace wayyayi nake so ba irinki yar kauyeba.

Kafin Hameeda tayi yunk'uri fitsari ya soma gan-garowa, don tagama tsurewa.
"Mtss yasaki saki ya mata wani mugun kalo ta fita.

Hameeda ta sauke ajiyar zuciya, a fili tace"mtss mugu kawai, an fad'a maka nima sonka nake. Yanda biyya zakayi nima haka biyya zanyi, kuma zana iya cewa su Mum bazan bi umurni su ba. Ji duk yasa na saki fitsarin da ba shiri Mungu kwai.

Areef hankalinsa in yayi dubu ya tashi, ya kira waya Teemah ya fi sau a k'irga, daga k'arshe ma sashi tayi a black list. In ya kira baya shiga.
Washe gari da yamma na bufi gidan su Teema ko da ya aika yaro, tace ace inji waye?. Yaron yazo ya fad'amasa, Areef yace" kaje kace inji Areef ne.
Ko da yaron yadawo yace" wai tace bata nan. Ido ya zaro ita ta fad'a maka "eh! Haka tace.
"Ok! Nagode"
Ya kai kusan minti talatin a qofar gidan bata fito ba, ga wayarta yaki shiga. Cike da dawuwa ya nufi gidansa. Fiskan nan ba annuri kamar an aiko masa da mutuwa.

       
                     Urs
         🎋S💖B🌲R💕
            (Triple Writers)📝

    [Truncated by Whatsapp]

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts