[23/5/10:00am]
🎋SADEEY S ADAM🎋
&
🌲RASH KARDAM🌲🌲
WITH
💖BEEBAHLUV💖💖
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
MA'YAUDARAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
20~23
Haka dai ya isah gida ya rasa me ke masa dadi,, wai meke shirin faruwa dashi ne?? Wadda yake bala'in so yake tunanin zai aura GA yadda take mishi,,, tun tana kin daukan wayar shi, yanzu har takai su ga yaje gidan su ta aiko tace mishi wai bata nan, haba teemah why,, kinsan yadda nike son ki kuwa,kinsan yadda nike jin ki a raina kuwa, gaskia Indai ban aure kiba ban jin zan auri wata,, koma na aura sai dai kawai in dole akai mun, kuma badan ina sonta ba. Areef kam abun yayi yawa ya dawo kamar mahaukaci duk ya hargitsa gidan, yana kwance kamar mutum mutumi shi ba me rai ba ba kuma marar rai ba.
A haka farouk yazo ya same shi,, a rude ya karaso yana kiran sunan shi, Areef meke damunka, meya faru dakai??
Bai ma san yana yi ba sai da ya taba shi sannan ya dago kai ya kalle shi, idon nan ya rune kamar gauta. Wai meke damunka ne?? Kalli yanda ka koma kalli yanda kake cikin gida duk yayi kaca2, haba Areef yanzu kai kullum baza kaima kanka fada ba, kullum cikin tunani haba, ya karasa maganar yana karaso wa kusa dashi.
Yana zuwa ya dafa kafadar shi, yaji gaba dayan jikin shi yayi zafi sosai, har karkarwa yake, yace subhanallahi ai zazzabi ne a jikin ka, kafin ya yi wata maganar ya kara amai.
Innalillahi ya fara ambatowa, yayi saurin daukan waya ya kira abokin su Dr Marwan yace gashi nan zuwa yanxu,, minti kadan ya iso,,
Yana zuwa ya fara gwada shi, nan dai ya daura mashi ruwa ya hada da allurar bacci. Sannan suka fara tattaunawa akan lamarin, ya akai hakan ta faru ne farouk? Whl nima yanzu nazo na tarar dashi haka.
Dazun dai munyi waya yace yana gidan su, daga nan kuma zai wuce gidan su teemah yanzu haka yaje tayi masa wani rashin mutuncin ne,, ya dawo zai kashe kanshi a banza,,.
Ni whl yarinyar nan ta isheni whl, ba son shi take ba, kawai wahala take bashi nayi mishi bayani har na gaji, kullum ina taya shi adduar Allah yasa ya gane kawai yaudarar shi take, in tana bukatar kudi a lokacin ne yake mutum a wurinta inya bata kuma sai ya zama dan iska.
Ga maganar hameedah kuma, da mum tayi mashi, akan hada su aure yace shi bai san zance ba sai dai wannan kwanjamammiyar me kama da......
Mwsttt tsaki Dr Marwan yayi, yace gaskia ya kamata yayi ma kanshi fada don kuwa yawan tunanin da yake zai haifar mashi hawan jini,, gashi nan BP din shi yayi high.
Yanzu ya kake ganin zamu shawo kan matsalar abokina,, ehh toh yanzu dai bari ya tashi muji meye silar shi wannan ciwon tukun sai mu san abinyi, but is difficult to him ya daina son wannan yarinyar sai munyi da gaske, shu'uma ce ta karshe.
A bangaren Hameedah kuwa, ta shiga dakin su da saurin ta gudun karta ci karo da wani, ga kaya jike na fitsari, tayi saurin komawa don gyara wurin, bayan ta dawo dakin ne sai ga hafcy ta fito daga toilet, yadai sis Hameedah ya kukai da yaya ne? Hmmm bari yar uwa, bari dai na shiga toilet tukun na fito.
Wanka tayi baki daya sannan ta fito daure da towel,, hafcy ce ta fara magana ai nasan dana tsaya yaya a akaina zai huce, kai yaya mugu ne whl. Hmm yo ai bayan tahowar ki kinji2 yanda mukai dashi,, kinsanni kuma da tsoro kamar farar kura, harda fitsarina a wando..
Habawa su hafcy an samu abinda ake so, nan ta fara tuntsira daria harda su hawaye, kice kinyi tawa kenan ai gaskia yaya akwai mugunta. Ai sis gaskia in aka hada auran ku da yaya an cuce ki, don kuwa in baki wasa ba har dukan ki zai ringa yi, whl kawai kice baki son shi, don karma a hada ku a cuce ki, ga masu son ki nan sosai kawai a wani hadaki da wannan mugun...
Hameedah ta share kwallar data gangaro mata,, tace to ya zanyi hafcy, kinsan bazan taba iya kallon fuskar mum ince ce bani son danta ba, in nayi haka nayi butulci,,, kedai ki taya addua in auren alkhairi ne Allah ya tabbatar mana dashi, in kuma babu toh Allah ya tarwatsa abun da gaggawa,,, ta taso ta matso inda take zaune ta share mata kwallar idon nata, tace toh sis zan taya ki addua, ki daina kuka Allah yana tare damu insha Allahu komai zaiyi normal, kinji matar yaya tayi mata gwalo na wasa.
Tayi daria sannan ta kai mata dukan wasa,, haka suka ci gaba da hirar su har lokacin sallah yayi..
Teemah ce zaune a parlor ita da ummanta,, Fatima tace na'am umma ina son in gaya maki wata magana, tace toh umma ina jinki akan yaron nan Areefu, dazun duk naji abinda kikai, kuma bai kamata ba bai dace ba abinda kikai,, yanzu ke bazan taba gaya miki mgn kiji ba ko? Yaron na yana sonki tsakani da Allah, auran ki yake son yi gashi dan kirki, dan gidan mutunci, amman kin watsawa idon ki toka kina mashi wulakanci,, kina biyewa kawayen zamani kece can kece nan duk kuna ganin burgewa ne toh whl ba burgewa bane, duk sanda damar da kika samu ta wuce ki toh whl ki kuka da kanki, ba baki nike miki ba amman kiyi hankali da rayuwar nan, namiji badan goyo bane zasu kaiki su baro ki, kullum ina gaya miki kiyi hankali da rayuwa..
Yaron nan kiga irin dawainiyar da yake dake, kee bama ke kadai ba harda mu, kullum baya gajiya wa kullum cikin faranta mana rai yake,, badon komai ba don saboda yana son ki,, umma kam harda kukan ta tana cewa tun bayan mutuwar mahaifinta ta chanza rayuwa, ba a isa a gaya mata taji ba kullum cikin fitina take Allah dai ya shirye mun ke yasa ki gane amin.
Nan dai umma tayi2 mata fada da nasihohi masu ratsa jiki, kamar ta dauka ta wani langwabe, umma kiyi hkr zan gyara hali na insha Allahu...
Areef bai tashi ba sai bayan sallar maghrib,, ya farka ya tashi da mika da salati, yaga drip daure a hannun shi sai farouk a gefen shi, Dr Marwan yaje ya dawo,, sannu Areef ya jikin naka, yace da sauki,, bari ya karasa sai cire kaje ka samu ka watsa ruwa zaka fi jin dadin jikin naka yace toh, ina Marwan yaje asibiti ya dawo ok..
Nan ya fara tariyo duk abinda ya faru,, hmm yace farouk yace yadai menene ah ba komai, naji kace hmm ne ai, yanzu kai ba zaka daina wannan tunanin bako? Farouk ai tunani dole ne ayi shi,,, bari in cire maka naga ya kare drip din sai kaje kayi wankan ga abinci nan.
Bayan ya shiga wankan ne, sai ga Marwan ya dawo,, a ah ya tashi ne ehh yanzu ya tashi, ok amman ya jikin nashi? Da sauki sosai gaskia ba kamar dazun ba, ok toh Alhamdulillah.
Bari yaci abinci sai mu tattauna akan matsalar, ok farouk yace.
Urs
🎋S💖B🌲R💕
[truncated by WhatsApp]
0 comments:
Post a Comment