New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE-24-25

[23/5/ 02:17PM]

💖BEEBAH LUV💖
            &
🌲RASH KARDAM🌲
             WITH
🎋SADEEY S. ADAM🎋

   🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
     MA'YAUDARAH
       🌺🌺🌺🌺🌺🌺

2⃣4⃣-2⃣5⃣

Bayan ya fito daga wanka bai saka wasu kaya masu nauyi ba Kawai doguwar Riga ta barci ya zura tare da feshe turare a jikinsa.

Still maganar teemah suke tattaunawa shida farouq,har yanxu yak'i yarda teemah yaudararsa take.
          Suna cikin jayayya marwan ya shigo "malan ko ka yarda ko ka k'i yarda yarinyar Nan ba sonka take ba,tsabar yaudara ce Kawai" yana fad'a ya Shige toilet, "hmmmm" Kawai Areef yace.

Tashi sukayi suma sukayi alwallah, farouq ya Yi musu jam'i suka gabatar da farali...

Farouq ya kalli marwan yayi smiling"Marwan kalli yadda abokinmu ya rame a yini d'aya kacal,gskya Areef kayiwa kanka fad'a ka nutsu ka gane teemah ba k'aunarka take ba,ka rungumi Hameedarka itace tafi dacewa dakai,itace baxata tab'a yaudararka ba".

"hmmm nidai ku bani shawarar yadda xan janyo teemah gareni bawai Kuna min mgnar wannan kidahumar ba,idan baxaku shawo kan matsalar Nan ba to ni kubarni dan xan iya komai dan ganin na auri teemah", "hmmm aikam baxaka auri wadda xata wulak'anta mana Kai".

Hka dai sukai ta lallab'a Sa amma ya dage sai teemah,har dai suka gaji suka zubawa sarautar Allah ido...
   
10:30pm ya raka su har bakin motocinsu,sukayi sallama kowa ya Shige  motarsa yaja....

   Kwance yake akan gado ya rasa abinda ke masa dad'i tunani kala2 yake akan teemah,shin so take Yi masa ko k'i??,amma har bacci ya d'aukesa bai samu amsar tambayar ba.

               *********

"Dan ubanki xo Nan" jikinta na tsuma ta matsa kusa da ita tare da fad'in "Aunty kiyi hkr dan girman Allah ki taimaka ki ceci rayuwata", kamota tayi tafara dukanta da hannuwanta gaba d'aya ta saki jikinta akanta sai kima take
        Tun tana ihu da salati har muryarta ya dashe,sai da ta gama Yi Mata lilis sannan ta saketa ta koma gefe tana huci...
        Rufaida nanan kwance tana numfashi sama2 jikinta kuwa duk Scars ne na duka da takesha kusan kullun...
        Aunty Farha kuwa tana gefe sai bala'i take,can tasa k'afarta ta hankad'a Rufaidah sannan tace "duk saurayin daya k'ara zuwa ya d'aukeki a Mota Kika k'i yarda kuje inda yakeso ko kuma ya buk'aci Abu a wajenki kika k'i basu had'in kai,idan suka kawomin complain a kanki wlh Sai na lahira ya fiki jindad'i,ke bakya ganin yadda samari ke kashewa 'yan matansu kud'i?Sai ke uztaziya ko?to wlh kad'an Kika gani,duka kuwa yanxu Kika fara sha indai bazaki na nemomin kud'i ba,
ke ko kunya bakyaji kullun kina zama da Kaya kala biyu da uban hijab kamar matar malan?to ko 'ya'yan masu kud'in sun gane bare ke da bakida uban kowa nid'in dai dani kike tutiya".
      Rufaidah dai batace komai ba jikinta ne keta azabar xafi da rad'ad'in ciwo,,amma ba tausayi Aunty Farha ta jata ta hankad'ata waje, "karki dawo min gidan nan ba tare da kud'i ba,hkrina ya k'are duk kyaun nan naki ace kin kasa yin amfani dashi?to bazai yuwu ba kullun in ciyar in shayar in miki sutura duk ni kad'ai ko tausayina bakyaji,to na gaji duk inda kud'i yake ki nemo sakarai kawai".

Tura gidan tayi tabarta a kwance a k'asa,batada da Wani gata,'yan unguwa dake taimakonta sun gaji dashan zagin Aunty Farha,yanzu ko kasheta Aunty zatayi babu mai cetonta Sai Allah...
    Haka ta tashi da kyar dan jikinta duk ciwo yake ga yunwa,rabonta da abinci tun na safe...
               Gabas kawai ta dosa Tana tafiya Tana d'angashi bata masan Ina xata nufa ba.

                 Urs...
            🎋S 💖B 🌲R
            (Triple writer's)


[Truncated by Whatsapp].

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts