New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE 26-30

[25/5/ 09:09PM]

🌲RASH KARDAM🌲
             &
💖BEEBAH LUV💖
          WITH
🎋SADEEY S. ADAM🎋

  🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
     MA'YAUDARAH
     🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

2⃣6⃣-3⃣0⃣

A bakin titi ta zauna tare da saka kanta tsakanin cinyoyinta.
     kuka takeyi sosai Yau ya xatayi ina zata dosa a cikin wannan dare???

Tana nan zaune motoci sai wucewa suke babu Wanda ya damu da rayuwarta bare ya tsaya...

"hello! Lafiya kike zaune Anan ko dai bamai hnkli bace"?,,d'agowa tayi ta kalleshi sannan ta mik'e tsaye a tsorace
     'yam Mata lfya kike zaune a Nan da wannan duhun dare,idan bakida gurin kwana ai za'a iya taimaka Miki amma bai kamata ki zauna Anan ba"...
        Kallon sama da k'asa tayi masa,tsoho ne dan daga gani ya doshi shekara hamsin
            "bana buk'atar taimakonka kaje nagode", bata tsaya Jin amsarsa ba taja d'angalalliyar k'afarta tayi gaba,,,ko taku uku batayi ba taji an janyota da k'arfi tareda hankad'a ta cikin mota...

Kafin ya rufe motar cikin k'arfin hali ta fito duk da bata iya taka k'afar sosai amma batasan lokacin da ta tsallaka titi aguje ba bata Kai ga tsallakesa duka ba taji mota ta bugeta k'ara ta saki tare da zubewa k'asa sumammiya.........

A d'imauce farouq yayi parking tare da nufowa inda take.
  torch d'in wayarsa ya kunna ya haskata,,mutanen da suka ga anyi abin a gabansu tuni sun iso wajen,wasu ma wucewa sukaxo Yi but duk sunyi parking abin hawa...

    "Malan mutun ka kad'e amma kake dariya" wani na kusa dashi yayi masa mgna.
        Farouq ya d'ago yana smiling"ban kad'e taba nadai kusa,shocked ta samu shiyasa har ta sume amma ban kad'e taba wlh", "ya kamata ka kaita asibiti dan kuwa kamar Bata motsi..
     Baiso hkan ba amma babu yadda zaiyi haka ya d'auketa ya shigar da ita mota babu Wanda yace zai bisu asibitin shima bai nemi hkan ba yaja motarsa yayi gaba

Direct gidansu ya nufa,yana Shiga yayi parking a harabar gidan sannan ya fita xuwa cikin gidan.
    A parlour ya samu mum d'insa da sisters d'insa Hidaya da Zulaihat,"yawwa ku biyoni mota ku karb'i sak'o" ba musu suka bishi...
     da kyar suka yadda suka d'auketa xuwa cikin gidan
  A bedroom d'in mum aka zubeta tsakiyar gado,har lkcin a sume take numfashi kad'ai zaisa ka gane tanada rai...

Ya basu lbrin abinda ya faru,dariya sukai tayi zulaihat kuwa har k'asa takai dan dariya..
  Mum ce tace a barta ta huta kar a tada ta,xuwa gobe ita xata rakata har gidansu
          cikin zolaya Hidaya ta kalleshi "su yaya an sama mana Aunty,kace mu fara shirye2 biki", "ke xan fasa Miki baki wlh,me xanyi da wannan 'yar k'aramar yarinyar gata xubin 'yan k'auye,ki k'ara tsokana ta ki gani idan ni sa'ankine",
    Mum ce ta harareshi tare da fad'in "idan har Bata burgeka ba taya ka gane tana da xubin 'yan k'auye,kayi Mata kallon k'urilla ko"?, god forbid" ya fad'a tare da barin d'akin...

            *************
Teemah ta d'ago ta kalli Futha "Kai duk Wanda ya samu dama sai ya dama,yanxu fa kalli daular da hydar ke sakarmin,na yarda da hausawa da suke cewa duniya gidan dad'i",
   "hmmm I pity ur lyf duk sanda Allah ya tashi kamaki kuma idan duniya gidan dad'i ce ai wata rana takan zamo gidan wahala",
     "Futha bansan yaushe xaki waye ba duniya tasan ki,na rasa gane kanki", kinga teemah ni ba wannan mgnar ta kawoni ba,ki shirya ranar Saturday za'a kawo kayan engage".

Dafe k'irji teemah tayi sannan tace "Futha Aure?ki rufawa kanki asiri tun kina yarinyarki a Maida ke tsohuwa,haha besty da hnklinki xakiyi aurennan", "ras kuwa,ke kuma ki tsaya ki gama cin duniya da allura bama tsinke ba,kinga na tafi dan kuwa inada abinyi" tashi tayi ta fita,da gudu teemah ta bita tare da fad'in "ki tsaya mu gama mgnar mana".


            Urs....
       🎋S 💖B 🌲R
      (Triple Writer's)




[Truncated by Whatsapp].

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts