[16/5/8:30pm.]
💖BEEBAH LUV💖
&
🌲RASH KARDAM🌲
WITH
🎋SADEEY S ADAM🎋
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
MA' YAUDARAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
06~10
Note: Pls fans, sakamakon jin da mukai anyi novel me suna YAUDARAH, shi yasa muka chanxa ma namu suna ya koma MAYAUDARAH,. Tnx
Sun isa babu dadewa, don daukan Futha, su tafi batai tunanin wani ne zai kai su ba, tayi tunanin a keke napep zasu tafi, daman bata shiga ba a kofa ta tsaya tayi mata waya, futha tayi ma ummanta waya sallama, tace sai sun dawo Allah ya kiyaye hanya, su gaishe da Amaryar tace toh.
Bayan ta futa ne ta gansu a cikin mota, ta shiga da sallamar ta, ta gaisar dashi daga nan bata sake cewa komai ba, sai dai in teemah tayi mata magana takan bata amsa a takaice, don Futha akwai kamun kai.
Bayan sun isa shima da zata futa tace mashi sai anjima, kai wannan kawar taki akwai ta da girman kai, sai wani shan kanshi take,, ayya whl baka fahimceta bane haka take bata fiya magana ba,,, ok sai yaushe zanzo daukar ki, tace zadai muyi waya ok sai ltr din kenan, ok bye.
Hmmmm kedai teemah bazaki taba jin magana ba, kullum cikin kula samari kike, wannan kuma daga ina kika kwaso shi,, daga ganinshi ba mutumin kirki bane,, don Allah teemah ki ringa tunani whl wannan rayuwar ba mai bullewa bace, ki nitsu kiyiwa kanki fada pls kinji kawata, ta kama hannunta, toh naji matar liman zanyi, ni muje dallah.
Matar soja kam ba karamin dadi taji ba,, tayi masu tarba me kyau,, sunci sun sha, sunyi hani'an.
Nan kuma aka dosa hirar school, after nan kuma aka fara ta samari, kowacce na bada nata lbrn, da irin yaudarar da take ma samari,, hmm nan fah teemah aka soma fede biri harda wutsiyar sa, ai duk naku wasa in gaya muku, nifa yanzu indai zan fita unguwa to alkawari ne sai nayi saurayi, kuma daman in naga kalar ka batai mun ba ko sauraranka bazan yiba, don kunsan ni sai mai kudi,, gwara wanda zan wanke shi, ba wanda zaizo yana mun karyar baya dashi ba.
Heeeeh whl kuwa yar uwa kinmin daidai, don kuwa yanzu sai da hakan inji Sumayya Gireii, don kunsan suma fa mazan yanzu dan karan yaudara ce dasu, yo kun manta ni da Ahmad ya yaudaran yazo ya kawo kudin aurena, ashe ba iyayen shine na kwarai ba, na karya ne tsabar yaudara ce irin ta maza,, ai shiyasa yanzu na Daura damarar yaudarar maza son raina, don nama daina tunanin aure yanzu, sai na gama cin dunia ta da tsinke tukunna.
Futha ce da ummilele suka gyara zama, hmm yanzu kukam kuna ganin hakan yafi maku ko? Whl kuyi ma kanku fada yaudara babu kyau, gwara ku tsaida guda daya nagari, yanzu dunia ta lalace, wasu samarin fa ba sonku suke tsakani da Allah ba, sai dai su zo su kashe muku kudi, in sun samu abinda suke so a gurin ku su gudu su barku, ai kuwa sun cuci rayuwar ku.. Whl kuwa fada musu ummi don kullum sai na gayawa teemah ta daina amman gani take burgewa ne, whl ba abin burgewa bane kuna cutan kanmu ne...
Can kuma rash ta amshe chab wai wa'azi zukuyi mana?? Ai gwara ma ku daina, don yanzu kam bazai shige mu ba, yanda ake yaudarar mu, muma sai mun dana, donni inda aure kazo mun ma tuni nike korar ka don ban shirya ba, sai na tatsi na tatsa son raina, in baka red card,, dakyau kawata ban mu kashe,,, inji sadeey, ai sai da hakan, don ni yanzu akwai me sanya mun credit, akwai me siyan kayan make up,, akwai me sai mun anko, akwai kuma driver na wanda duk inda zanje shi yake kaini,, kuma duk yanda nace ana yi mun, koya kika ce kawas,, kwarai kuwa,,
Matar soja tace ayi dai a hankali don kuwa a wannan zamanin ba kasa fai samari ke bama yan mata kudi haka kawai ba, sai kema in kina bada gudummuwa,,
To ai ba wani abu bane baya wuce shan minti, kawai meye a ciki don an dan sha minti ai ba wani abu bane inji teemah duk teemah tafi zaqalqalewa a cikin su don kuwa idon ta ya bude sosai sai dai gyaran Allah kawai...
Ai kuwa whl wani abu ne babba ma kuwa don kuwa kunsan babu kyau Allah ya haramta hakan,, kuma sai sun gama shafe ku sannan su arce su barku anan, su kara wuta, wani ma daman da matar shi, wani kuwa da wadda aka sa musu rana, tunda yaga kin sakar mashi sai yazo yayi abinda zai yi ya gudu, Allah dai ya kara shirya mana zuri' a amin..
Ohoo sudai ina ai wanda yayi nisa yayi nisa, sai dai gyaran Allah kawai Allah ya gyara amin.
Sai dab da maghrib suka tafi ansha hirarraki kala kala..
💐Wacece Teemah💐
Teemahluff diya ce ga Alh Rislan da Haj Raudha, Alh rislan haifaffan garin kano ne a wata unguwa da ake kira Hotoro Dan Marke,,, malamin makaranta ne govt, sec, school dake hotoro, ya dade yana teaching, har ya samu mukamin principal a makarantar.
Alh rislan mutum ne me kirki da kawai ci, da rikon a mana, da sanin ya kamata,, baya karbar cin hanci, yana da bala in kirki da rikon addini..
Matar shi daya, raudha me bala'in hakuri da addini, yayan su uku Fauzan, shine babba sai Teemah itane ta biyu, sai kuma mukhtar shine autan su.
Sun taso cikin gata da tarbiyya, don kuwa Alh rislan yana kokari Sosai wurin basu tarbiyya da ilimi, both side, islamiyya da boko, yana son yaga sunyi karatu me taho, farko sun fara govt school daga baya ya cire su ya saka su a private school tun suna primary 4 suke Private school har secondary school.
Yana bala'in kokari duk abinda ya samo akan iyalin shi suke tafia, ba wani me kudi bane rufin asiri ne kawai da zuciyar nema.
Akwai wani makwocinsa Alh Faisal yana da kudi sosai,, kuma suna shiri da Alh rislan don kuwa shike bashi shawara, ya zama kamar dan uwan sa,, yakan taimaka mashi sosai bawai don ya gaza bane a ah yana dai taimakon shine tunda ya fishi kudi nesa ba kusa ba.
Akwai wata shekara ya hada da nashi iyalin da Alh rislan da raudha ya kai su aikin hajji,, shi yasa ake kiransu Alh rislan da haj raudha..
Alhamdulillah komai yana tafia daidai a rayuwar gidan Alh rislan, su teemah da Fauzan har sun sauke Qur'an don ba wani tazara ke tsakanin su ba, shekara daya ne tsakanin su.don haka komai tare suke yi, hatta a school ma aji daya ya bata, kuma shi baya da jikin girma, ita kuwa tana da tsaho ana yawan cewa ita ce babba akan shi..
Teemah ta tashi cikin tarbiyya da nitsuwa tun tana Karama amman tana shiga SS1 a school ta zama fitinanniya kamar ba ita ba,
Don kuwa yan mazan ajin su da yan matan ma yawancin su duk kangararru ne yayan masu kudi, shi yasa fitinar tayi yawa, su suka bata tarbiyya teemah,, tun tana kin biye musu har dai ta fara shiga layi.
A lokacin bata wani kware ba, kuma bata kula samari don bata fara zuwa zance ba, babanta yace karatu zatai har sai ta fara higher institution sannan zai aurar da ita don yana son yaga sunyi karatu, tunda sun sauke na muhammadiyya, kuma yasan yarsa tana da tarbiyya zata rike mutuncinta a duk inda take.
Ayyah baba rislan kayi kuskure don kuwa,, abokai da kawaye sun lalata maka tarbiyyar da ka dade kana yi tun fil'azal, teemah kam ta fara nisa yanzu sai dai gyaran Allah.
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah su teemah har an gama secondary school, kuma Alhamdulillah tayi passing exams din ta gaba daya, a waec neck ne tayi losing subject biyu. Tana da kokari sosai da maida hankali sai dai kawai rashin jin da ta zunduma kanta yanzu a ciki,,.
Bai wani bata Lokaci ba ya samar mata admission a Bayero university, kuma ta samu a fannin sociology, yayi mata fada sosai akan ta maida hankali akan abinda ya kaita baya son kula yayan banza, tayi abinda ya kaita tace to kamar da gaske..
Shi kuwa fauzaan yana ABU ZARIA can ya sami admission shi kuma mukhtar Auta yana JS one don akwai tazara tsakanin shi da teemah.
Su teemah abu sai kara yawa yake, don kuwa ta kara haduwa da qawayen banza, yanzu har party suke zuwa, gashi duk saurayin daya ganta da wuya baice yana sonta ba.
Tana level 2 Allah yayi ma Alh rislan rasuwa, sunyi babban rashi,,, sunyi kuka sosai, a lokacin teemah kamar ta shiryu bayan kwana biyu kuma aka koma ruwa....
Alh Faisal kam ya rike zumunci, don bai yarda su raudha ba, yana taimaka masu sosai duk wata yakan sai masu kayan abinci ya aika masu. Kuma yana shiga har gidan yaga lfyr su, ana yawan kai mashi zancen teemah tana yawan tara samari, yana iya bakin kokarin sa akan ta, amman abun yaci tura sai dai addua.
Wata ranar juma a ce ta dawo daga school, suka hadu da Areef a bakin titi tana jiran mota, yayi parking ya fito har wajen da take yayi mata sallama ta amsa, bayan nan ne yace ina zata tace gida ta tashi daga skul ne, yace in ba damuwa tazo ya sauke ta,,, hmmm daman take jira taji yace, don ta ganshi da katuwar mota, tasan akwai money, don ita lashe money ce.
Bayan sun je ya karba number din ta yace zai dawo gobe sai su zauna su fahimci juna, tace tohm Allah ya kaimu sai yazo,, ta shige gida..
Areef kam ya kamu sosai don motsi kadan tunanin teemah shikam ya samu mata, a nasa tunanin don tayi masa..
Toh masu karatu ku biyo mu don jin yanda soyayyar teemah da Areef ta faro asali.
Urs....
🎋S💖B🌲R
(Triple Writer's).
[truncated by WhatsApp]
0 comments:
Post a Comment